Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 05.07.2020

Taskar Guibi: 05.07.2020

312
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha uku ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da aahirin.

1. Bari in fara da batun wutar lantarki wacce rabonmu da ita har mun manta. Tun kusan ranar laraba da suka dauke, haka muke yini haka muke kwana babu wuta, in har an kawo to gara ma ka kunna kyandir. Su makwabtanmu ma mai karfi aka kawo musu duk ta kona musu kayayyakin da suka jibanci lantarki wato laturonik.

2. Majalisar Dinkin Duniya na tunanin dakatar da ayyukanta na jinkai a Arewa maso Gabashin kasar nan saboda farmakin da ake zargin ‘yan Boko Haram sun kai wa wani jirgin sama na ayyukan jinkai a Damasak.

3. Sojoji sun ce sun ci gaba da kai farmaki ta sama, mabuya dabam-daban ta ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Barno.

4. Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da duk wani korafe-korafen da jam’iyyun siyasa suka kai gabanta da ke kalubalantar zaben gwamna Yahya Bello, kotun ta kuma tabbatar masa da shi ne zababben gwamnan jihar Kogi.

5. Matar gwamnan jihar Binuwai, da dansa, da shugaban ma’aikatansa na fadar gwamnatinsa da sakataren gwamnatinsa, da shugaban ma’aikata na jiharsa duk sun harbu da kwaronabairos. Gwamnan ne kadai ya tsallake rijiya da baya bai harbu ba.

6. Gwamnan jihar Ebonyi ya harbu da kwaronabairos.

7. Hukumar Kwastam da ke Apapa a Legaa ta ce cikin watannin shida da suka gabata na shekarar nan ta tara naira biliyan dari biyu da ashirin da bakwai.

8. An dawo da wasu ‘yan Nijeriya su dari biyar da ashirin da biyu daga Amurka.

9. ‘Yar wasan nan Funke da aka fi sani da Jenifa da mijinta, sun je kotu don neman duba hukuncin da aka yanke musu saboda wata dabdala da suka shirya ta bikin zagayowar ranar haihuwa a lokacin kulle, har da kai ga kamata, da yanke mata hukunci.

10. An tura karin ‘yan sanda jihar Zamfara don tabbatar da tsaro.

11. Jiya kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari shida da uku, a jihohi da alkaluma kamar haka:

Lagos 135
Edo 87
Abuja 73
Ribas 67
Delta 62
Ogun 47
Kaduna 20
Filato 19
Oshun 17
Ondo 16
Inugu 15
Oyo 15
Barno 13
Neja 6
Nasarawa 4
Kabbi 3
Kano 2
Sakkwato 1
Abiya 1

Jimillar wadanda suka harbu 28,167, wadanda suka warke 11,462, wadanda suka riga mu gidan gaskiya 634, wadanda ke jinya 16,071.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Shekaranjiya Allah Ya yi wa malamina Malam Hanisu Lawal rasuwa aka yi jana’izarsa jiya da safe. Malam Hamisu Lawal ya koyar da ni TEACHING METHODS a karatun difiloma da na yi na koyon aikin malanta, na jami’ar gwamnatin tarayya da ke Minna, a reshenta da ke kwalejin foliteknik ta Kaduna a shekarar dubu biyu da bakwai, bayan na kamnala digirina na biyu a shekarar 2006, kuma shi ya duba ni a lokacin aikin binciken da na yi bangaren na koyarwa. Malam Hamisu Lawal bai dade da yin ritaya daga kwalejin foliteknik ta Kaduna ba a matsayinsa na malamin da ya kai kololuwar aikin koyarwa wato CHIEF LECTURER. Sai mu ce Allah Ya jikansa, Ya yafe masa kurakuransa, ya raya zuri’ar da ya bari, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin. Haka nan Allah Ya yi wa mijin abokiyar aikinmu a kwalejin foliteknik ta Kaduna Mrs Binta Abdulraman rasuwa shekaranjiya. Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Shi ma Allah Ya jikansa Ya yafe masa kurakuransa, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply