Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 06.10.2020

Taskar Guibi: 06.10.2020

374
0

Assalamu alaikum barkanmi da asubahin talata, goma sha takwas ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Oktoba, shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Da yake jiya ce ta kasance ranar malaman makaranta ta duniya bakidaya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba malaman makaranta mamaki saboda ya amince a musu sabon tsari na albashinsu. Na biyu daga yanzun malamin makaranta sai ya shekara arba’in yana koyarwa kafin ya yi ritaya, ba talatin da biyar da ake yi a baya ba. Sannan sai malamin makaranta ya kai shekara sittin da biyar a duniya yana koyarwa kafin ya yi ritaya, sabanin a da, idan ya kai shekara sittin a duniya dole ya yi ritaya. Sannan ‘ya’yan malaman makaranta sun daina biyan kudin makaranta, kuma garanti ko otimatik ne ‘ya’yan za su samu makaranta. Haka nan daga yanzun dalibai da ke karatun koyon malanta, suna gama makaranta za su samu aiki wato za a dauke su aiki.
Wadannan su ne albishir da shugaban kasa ya yi wa malaman makaranta. Amma fa wadanda ke koyarwa a firamare da sakandare.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya hana ‘yan sandan nan na musamman da ke yaki da fashi da makami wato F-SARS sintiri a tituna saboda tuhumarsu da ake yawan yi suna cin zarafin jama’a kamar dabbobi. Shi kansa Osinbanjo mataimakin shugaban kasa ya yi tir da halayen wadannan ‘yan sanda da ya ce ba su da imani ko kadan.

3 . Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude wani taro na yini biyu na kyautata fahimtar juna tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa.

4. Gwamnatin Tarayya ta ba hukumar kidaya ta kasa naira biliyan goma domin aikin fitar da bangarorin kidaya na kananan hukumoin kasar nan.

5. ‘Yan sandan jihar Kano sun kama matar da ta kashe ‘ya’yanta biyu.

6. Shugabannin Arewa Maso Gabashin kasar nan sun goyi bayan agajin sujojin Cadi da Gwamna Zulum ya nema don taimakawa a gama da ‘yan Boko Haram.

7. Wasu mahara sun yi awon gaba da mutane da dama a Malamawa da ke yankin Jibiya da ke jihar Katsina shekaranjiya lahadi. Yankin da jama’a suka fito suka yi zanga-zangar sun gaji da satar musu jama’a da kashe su, ‘yan sanda suka kama masu zanga-zangar su wajen hamsin suka garkame. Fiye da sau hudu mahara na kai musu farmaki suna kwasar musu mutane, mata da yara har da masu goyo.

8. Dakaru sun kashe ‘yan bindiga su biyu a hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da samo makamai da ke tare da su.

9. Hukumar kula da al’amuran ‘yan sanda ta yi wa jami’an ‘yan sanda su 175 karin girma har da DCP Jimoh .

10. Hukumar kula da kiyaye hadurra ta kasa ta kai jami’anta su 1,500 da motoci 25 kananan hukumomi 18 na jihar Ondo da za a yi zaben gwamna ranar asabar mai zuwa.

11. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna dakon gyaran gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

12. Ma’aikatan jami’o’i manyansu da kanana, da malaman jami’o’i da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya suna yajin aiki. An ce malamai da sauran ma’aikatan kwalejojin foliteknik ne matsorata ba sa iya zuwa yajin aiki. Amma ba in ji ni ba fa. Ji na yi ana gulmarsu. Shekararsu daya da wata bakwai suna dakon ariyas na sabon albashi.

13. Albashin watan Satumba ya yi batar dabo ba shi ba dalilinsa, in ji yawancin ma’aikatan sashen ilimi na gwamnatin tarayya na kasar nan, irin su foliteknik da sauransu.

14. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 120 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Ribas 65
Ogun 9
Katsina 8
Anambara 7
Bauci 5
Oyo 5
Nasarawa 3
Kaduna 2
Kwara 1
Taraba 1
Imo 1
Delta 1

Jimillar da suka harbu 59,465
Jimillar da suka warke, 50,951
Jimillar da ke jinya 7,383
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,113

Mu wayi gari lafiya.

Af! Da yake jiya ce ranar Malamai, na ga tsofaffin dalibaina suna ta rubutu a kaina a fesbuk. Ban da irin su Jafar Jega da suka kira ni a waya jiya suna mun godiya da irin koyarwa da tarbiyyar da aka musu. Ga daya daga cikin rubuce-rubucen na kwafo na Anas Halliru Anas kamar haka:

‘This is Dr. Malam Ishaq Idris Guibi Guibi. He taught me Hausa as a language. He happens to be among the best teachers that I won’t like missing his class. He is a Teacher, A Journalist and a Consultant.
He is the CEO of Guibi Consultancy, currently a Lecturer in the Dept. Of Mass Communication and also Director of News and Current Affairs of Kad Poly FM.
Sir, may Allah reward you in Return.
Happy Teacher’s Day’

Sai dai ba na tare da rediyon Spider FM a yanzun, kuma na bar wajen a matsayin manaja ne don ba mukamin darakta a rediyon.

Anas Halliru da su Mujahid Abbas da Jafar Jega da sauran dinbin dalibaina da ke ko’ina a duniya ina alfahari da ku. Haka nan ni ma malamaina ina godiya.
Saboda su suka koya mun wannan rubutun da nake muku duk asubah kuna jin dadi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply