Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 06.12.2020

Taskar Guibi: 06.12.2020

431
0

Assalama alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga Disamba, shekarar 2020.

1. Ana kyautata zaton ranar Alhamis mai zuwa idan Allah Ya kai mu shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hallara gaban Majalisar Wakilai amsa gayyatar da ta masa, ta ya je ya yi bayanin me ke damun matsalar tsaron kasar nan.

2. Labari na ta karakaina a soshiyal midiya Janar Buratai, na gargadi ga sabbin janarorin soja da aka kara wa girma cewa, yanzun ba a yayin juyin mulki.

3. Hukumar Zabe ta Kasa ta gudanar da zabuka na cike gurbi a sassa daban-daban na kasar nan.

4. Mutanen Jihar Barno sun yi korafin sun fi so Shugaban Kasa ya je da kansa jihar don yi musu ta’aziyyar manonan da aka yanka, ba wai ya tura ‘yan aike da sako ba.

5. Wajen wata takwas ke nan daliban jami’a na gida suna zaman kashe wando, sakamakon yajin aikin malamansu, da har yau da sauran rina a kaba, tsakanin Gwamnatin Tarayya da Malaman na Jami’a.

6. BBC Hausa ta sanar da gwarazanta na bana su uku, na Gasar Hikiyata ta 2020 tare da karrama su da kudi DALA, da ba su hatimi na shaida. Kamar yadda na bayyana a rubutuna, ina cikin alkalan farko na hikiyar ta wannan shekarar, da muka duba rubutun hikiya ta mata fiye da dari hudu, muka tantance zakaru talatin cikinsu, wato kowanne alkali ya zabo goma ta la’akari da kwazon kowacce, sannan alkalai na karshe suka tantance suka zabo uku da suka yi zarra daga goma-goma da kowannenmu ya zabo. Wacce ta zama gwarzuwar shekara na cikin goma da na zaba daga cikin wadanda na duba.

7. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 310 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 128
Legas 86
Kaduna 26
Katsina 7
Binuwai 5
Edo 5
Jigawa 5
Ogun 5
Bayelsa 2
Kano 2

Jimillar da suka harbu 68,937
Jimillar da suka warke 64,650
Jimillar da ke jjnya 3,107
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,180

8. Tsohon Ministan Tsaro a zamanin gwamnatin mulkin soja ta Buhari 1984 -1985 Domkat Bali, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara tamanin a duniya.

9. Ma’aikatan kwalejojjn foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekarar da ke shirin kankama, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Sun dade suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta balle. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musualkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya Kidinafas suka kashe Sani Khalil Rigasa Kaduna, bayan sun karbi kudin fansarsa. Kisan da ya zama kusan babban jigon fesbuk a jiya da labarin kisan nasa ya bazu.
Ga daya daga cikin rubuce-rubucen da na gani jiya a kan kisan da suka yi wa Sani Khalil daga Ahmed Tijjani Ramalan:

“Breaking: Kidnappers Kill Rigasa Youth After Collecting Ransom

December 5, 2020
Voice of Liberty
Abdul-Azeez Ahmed Kadir

Kidnappers have killed the abducted Rigasa youth Sani Khalil who they took away after attacking them along the Airport – Train Station on 20th November, 2020 in Igabi Local Government Area of Kaduna State.

The kidnappers had demanded for 10 million naira ransom which the family said they could not pay, but rallied round to raise 1.5 million naira.

Family sources said the kidnappers asked them to meet them in Zaria where other family members of victims from Zaria and Yobe converged. The kidnappers then directed them to Galadimawa where they collected the ransoms. They then directed them to the victims.

The victims were said to be at a river where they tried washing up after their release, from nowhere four of the kidnappers appeared with guns and demanded for Sani Khalil.

On identifying him, they shot him dead and told others to tell his family that they killed him for wasting time in paying the ransom.

Other victims families from Zaria and Yobe State were said to have fled the place as they were refused to even carry his remains and the place is inaccessible by many.

At the time of this report, Khalil family and friends were still struggling to find ways to the place and how to convey his remains back to Kaduna for burial.

Khalil along Rabiu Auwal and Umar Elkhaddab fell victims of the kidnappers on 20th November, 2020 between Kaduna Airport and Rigasa Railway Station road when the gunmen attacked motorists after the time the last train from Abuja to Kaduna should have arrived.

Awwal and Elkhaddab escaped with gunshot wounds and were rushed to 44 Nigerian Army Reference Hospital where Auwal later died, succumbing to the gunshot wounds, while Elkhaddab survived and still recuperating from the gunshot wounds.

Khalil was however not lucky and was abducted after being shot.

Rigasa community with over a million population has been victim of kidnapping for ransom and killings, leading to citizens protesting to the State House of Assembly few months back.

The Kaduna – Abuja highway has witnessed many kidnappings for ransom and killings, leading to increase traffic at the train station as many travellers abandon the road for the fear being kidnapped or killed”

Allah Ya jikansa da duk sauran wadanda suka riga mu, Ya saka masa cikin gaugawa, mu kuma Ya ci gaba da mana katangar karfe da kidinafas Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply