Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 07.01.2021

Taskar Guibi: 07.01.2021

230
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, ashirin da biyu ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Da ta zama daidai sa shida ga watan Janairun 2021.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1,664 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 652
Abuja 407
Folato 160
Kaduna 83
Ribas 62
Adamawa 47
Nasarawa 38
Abiya 29
Edo 28
Anambara 27
Neja 24
Ogun 24
Imo 15
Oyo 14
Kano 12
Oshun 12
Barno 9
Delta 7
Inugu 7
Bauci 5
Ekiti 5
Sakkwato 5
Jigawa 2
Jimillar da suka harbu 94,369
Jimillar da suka warke 77,299
Jimillar da ke jinya 4,254
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,324

2. Kwaronabairos karo ta biyu, na ci gaba da watsuwa a kasar nan kamar ruwan dare, da wasu ke dangantawa da cunkoson da ake samu wajen rajistar samun lambar dan kasa.

3. Wasu ‘yan Nijeriya sun koka a kan tafiyar hawainiya da aikin rajistar samun lambar shaidar dan kasa ke yi.

4. Kungiyoyin kwadago NLC da TUC sun ce ba su yarda da karin kudin zama a duhu da aka yi ba.

5. Keyamo karamin ministan kwadago, ya ce ba da amincewarsu aka yi karin kudin zama a duhu ba.

6. Gwamnatin Tarayya ta ba bangaren sufurin jiragen sama, tallafi/bailout, naira biliyan hamsin da takwas domin su kacancana a tsakaninsu, don jajigewa daga abin da ya auku gare su a lokacin kulle na kwaronabairos.

7. Malaman jami’a na nuna alamun za su sake komawa yajin aiki.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello, ya ce shi fa ba zai sasanta da wani dan bindiga ko kidinafa ba. Don bai ga dalilin sasantawa da makasa da ke kashe jama’a da kona dukiyoyi har da dabbobi na jama’a ba.

10. Wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun je garin Wandeo na jihar Barno, suka jidi kayan abinci, da motocin jama’a da kona gidaje da shaguna, amma ba su yi wa kowa ko kwarzane ba, ba su kuma yi guzurin wani mutum ko daya ba, illa kaya.

11. ‘Yan sanda da sojoji a jihar Katsina, sun ce sun kashe ‘yan bindiga shida, a Kankara.

12. Wasu bayanai na nuna mahukunta jami’ar Bayero ta Kano, sun soke shekarar karatu da ta gabata, cewa ba a yi karatun shekarar ba kwata-kwata saboda yajin aiki da kwaronabairos da suka sa dalibai suka cinye shekarar karatun a gida.

13. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, don ga shi wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya kuma Allah Ya mana maganin kidinafas a duk inda suke Amin.

Af! Can a soshiyal midiya na tsintso wata raha a kan karin kudin zama a duhu da ake zargin an yi da ke cewa:

NERC: We didn’t increase electricity tariffs; we just adjusted the price, N2 to N4 per kWhr.

Na yi nan.

Is’haq IdrisGuibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply