Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 07.05.2020

Taskar Guibi: 07.05.2020

352
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha hudu ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fjyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Mayu, shekarar 2020.

1. Ma’aikatan kwalejojin ilimi, da na kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin ga azumi ya raba, yau goma sha hudu, watan Afrilu talatin da bakwai, watan Mayu bakwai, ba dilin-dilin babu dalilinsa. Ga kulle, ga zafi, wasu unguwanni ba wuta, wasu ba ruwa, ga cututtuka manya da kanana. Abinci ya kare, kudi ya kare, ka fita a maka tara, ka ci gaba da zama cikin gida ai ta rigima da iyali saboda babu. Fiye da shekara ana jiran ariyas shiru. Albashi gibi, wasu wawulo. Su ma malaman jami’a wata na hudu ke nan babu dilin-dilin babu dalilinsa. Bayan tun 23 ga watan jiya Baba Buhari ya ce a biya kowanne ma’aikaci albashinsa.

2. Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsarin da za a yi amfani da shi wajen alkinta kudaden da aka samu na gudunmawar yaki da kwaronabairos.

3. Yau da dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen Nijeriya ke karewa, gwamnatin Nijeriya ta kara tsawon dokar da mako hudu. Sai bayan wata daya ke nan jirage za su ci gaba da sauka da tashi a ciki da wajen kasar nan.

4. Jiya wuraren karfe takwas saura kwata na dare jirgin ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga Dubai ya iso Legas, a ciki har da wacce ta haihu. An ce kafin su taho duk an gwada su ba wanda ya harbu da kwaronabairos, kuma za a killace su a wasu otel-otel da aka ware don kara tantance lafiyarsu. Za a bi sauran kasashen irin su Ingila da Amurka da sauransu don kwaso ‘yan Nijeriya.

5. An kulle gidan talabijin na kasa da ke Katsina NTA Katsina sakamakon gano shugaban gidan ya harbu da kwaronabairos.

6. Ban da likitoci talatin da hudu da aka gano sun harbu da kwaronabairos a jihar Kano, a jihar ta Kano an gano ma’aikatan lafiya sun kai ashirin da hudu da su ma suka harbu.

7. ‘Yan kasuwar Kano sun yarda sun rage farashin kayan abin masarufi musamman sikari/siga.

8. Gwamnan jihar Katsina Masari ya nuna rashin jin dadinsa yadda duk da dokar kulle, ‘yan bindiga da kidinafas na ci gaba fitowa suna cin karensu babu babbaka a jihar.

9. A jihar Kaduna an gano almajirai sittin da biyar, da ‘yan sanda biyu da suka harbu da kwaronabairos. A dai jihar ta Kaduna, kidinafas sun kashe mutum daya, suka yi kidinafin mutum uku. A dai jihar ta Kaduna Gwamna El-Rufai ya ce an kashe naira biliyan biyu wajen rabon kayan agaji a wannan yanayi da aka shiga.

10. Asusun lamani na duniya IMF ya ba Nijeriya rancen/bashin dala biliyan uku da rabi ba ‘yan wasu mutsamutsai.

11. An kwantar da Sarkin Daura a asibiti, saboda lalura ta rashin lafiya da ake kyautata zatton kwaronabairos ce.

12. Gwamnatin jihar Kwara ta yi wa fursunoni arba’in da shida ahuwa.

13. Masu kare muradun tsohon shugaban mulkin soja marigayi Sani Abacha, na ci gaba da yada ayyukan da ya yi wa kasar nan masu yawan gaske kuma manya-manya a lokacin da yake mulki, daidai lokacin da ake ta batu a kan kudaden da aka maido da su kasar nan, da ake zargin ya kai can kasashen waje ya boye/adana.

14. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta ce sun yi nasara dakile yaduwar kwaronabairos a kasar kashi na farko. Ita kuwa Birtaniya cewa ta yi mutum dubu talatin ya riga mu gidan gaskiya a kasarta sakamakon cutar.

14. Kasar Madagaskar ta ba Nijar da wasu kasashen Afirka wani ganyen shayi da ke rigakafi da kuma maganin kwaronabairos, kodayake hukumar lafiya ta duniya ta ce ba a tantance gaskiyar aikin maganin ba tukuna.

15. Gwamnan jihar Bauci ya ce zai samar da takunkumi guda miliyan uku don raba wa ‘yan jihar.

16. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 195 ne kamar haka:

Legas 82
Kano 30
Zamfara 19
Sakkwato 18
Barno 10
Abuja 9
Oyo 8
Kabbi 5
Gwambe 5
Ogun 4
Katsina 3
Kaduna 1
Adamawa 1

Da ke nuna zuwa jiya da daddare mutum 3,145 ya harbu, 534 ya warke, 103 ya riga mu gidan gaskiya, 2,508 yake jinya.

Ga yawan da ke kowacce jihar da abin ya shafa:

Lagos 1308
Kano 427
Abuja 316
Barno 116
Gwambe 103
Katsina 95
Ogun 95
Kaduna 85
Bauci 83
Sakkwato 85
Edo 65
Oyo 52
Jigawa 39
Oshun 37
Zamfara 46
Delta 17
Akwa Ibom 16
Kwara 16
Taraba 15
Adamawa 15
Ribas 14
Kabbi 18
Ondo 13
Yobe 13
Ekiti 12
Nasarawa 11
Inugu 8
Bayelsa 5
Ebonyi 5
Neja 4
Filato 4
Abiya 2
Binuwai 2
Imo 2
Anambra 1

3,155 da suka harbu, a cire 534 da suka warke, a cire 103 da suka riga mu gidan gaskiya, saura 2,508 ke jinya.

Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.

Af! Jiya Al-Amin Saleh mai gidan talabijin na TAURARUWAR AREWA da ke watsa shirye-shiryensa ta intanet, ya kira ni a waya, ya shaida mun cewa an sa wanda zai dinga karanta rubuce-rubucen nawa na duk asubah a tashar tasu ta talabijin. Da ke nuna an samu karin gidajen talabijin da rediyo, da jaridu da mujallu, da dandali daban-daban, da daidaikun jama’a da kungiyoyi da ke yada/watsa labarun da nake bayarwa a kullum da asubah kai tsaye daga dandalina.
Dinbin godiya ga kowa da kowa, Allah Ya bar zumunci Aminci.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply