Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 07:06:2020

Taskar Guibi: 07:06:2020

135
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha biyar ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Yuni, na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Gwamnatin Tarayya ta kwace wani jirgin sama na hawa na tsohon ministan mai Dan Etietie a kasar Kanada da kudinsa suka kai dala miliyan hamsin da bakwai.

2. Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kawo shawarar a yi wa bangaren lafiya na kasaar nan garambawul.

3. Bankin Raya Afirka ya amince wa Nijeriya bashin da ta nema a wajensa dala miliyan dari biyu da tamanin da takwaa.

4. Kasar Masar ba ta yarda Okonja Iweala tsohuwar ministar kudin Nijeriya ta jagoranci hukumar kula da lamuran kasuwanci ta duniya WTO ba, kamar yadda shugaban kasa ya ba da sunanta ba.

5. Sojoji sun ce sun kashe ‘yan bindiga wajen saba’in a dajin Kaciya da ke jihar Kaduna.

6. Wasu kidinafas sun je wani gida da ke Gwanin Gora a jihar Kaduna ranar alhamis da daddare, suka tafi da mutum shida, cikinsu har da yaro mai shekara takwas.

7. ‘Yan sanda sun ce mutum goma sha biyu ‘yan bindiga suka kashe a harin da suka kai na baya-bayan nan jihar Binuwai.

8. Kungiyoyin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya na jihar Kaduna, sun kara wa gwamnatin jihar Kaduna mako biyu. Ko ta saurare su ta biya musu bukatunsu ko su yi yaji.

9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya, na nan suna korafin shekara daya da kusan wata biyu suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun wannan shekarar.

10. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbi da suka harbu da kwaronabairos mutum 389, a jihohi kamar haka:

Legas 66
Abuja 50
Delta 32
Oyo 31
Barno 26
Ribas 24
Edo 23
Ebonyi 23
Anambra 17
Gwambe 17
Nasarawa 14
Imo 12
Kano 12
Sakkwato 12
Jigawa 8
Ogun 7
Bauci 5
Kabbi 2
Kaduna 2
Katsina 2
Ondo 2
Abiya 1
Neja 1

Kowacce jiha taba da:

Legas 5729
Kano 997
Abuja 912
Edo 387
Katsina 387
Oyo 365
Barno 348
Kaduna 337
Ogun 336
Ribas 332
Jigawa 290
Bauci 285
Gwambe 201
Delta 148
Kwara 127
Sakkwato 127
Filato 113
Nasarawa 104
Ebonyi 103
Zamfara 76
Imo 59
Yobe 52
Oshun 49
Akwa Ibom 45
Adamawa 42
Neja 42
Ondo 40
Kabbi 35
Bayelsa 30
Inugu 30
Abiya 29
Ekiti 25
Taraba 18
Abiya 16
Binuwai 13
Kogi 3
Kuros Ribas 0

Wadanda suka harbu 12,233
Wadanda suka warke 3,826
wadanda suka riga mu gidan gaskiya 342
Wadanda ke jinya 8,065

Mu wayi gari lafiya.

Af! Talakawa har da wasu ‘yan majalisun dokoki na tarayya, na ci gaba da korafin daga bullowar kwaronabairos a Nijeriya zuwa yau mutum nawa ta kashe? Daga bullowar kwaronabairos zuwa yau nawa ‘yan bindiga suka kashe a jihohin Katsina, da Sakkwato, da Zamfara, da Kaduna, da Neja, da Binuwai, da Nasarawa, da Abuja da da da da da da da?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply