Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 08.01.2021

Taskar Guibi: 08.01.2021

257
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da uku ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumar sanya ido a kan masu kara wa talakan Nijeriya kudin zama a duhu, da ta sanya kamfanonin raba duhu da karbar kudin zama a duhu da sunansu ke kama da na ‘yan rawar banjo wato disko, su hanzarta janye karin kudin zama a duhu da suka yi kasassabar karawa, da suka ce za a soma biya daga daya ga watan nan da muke ciki.

2. Ma’aikatan hukumar yi wa ‘yan Nijeriya rajistar shaidar dan kasa, sun soma yajin aikin yi wa ‘yan Nijeriyan rajistar, saboda abin da suka kira, kokarin gwamnati ta sa su, su harbu da kwaronabairos daga jama’a da ke tirmitsitsin zuwa a musu rajistar, alhali ma albashinsu bai wuce cikin cokali ba, ga ba kula ake da jin dadinsu ba.

3. Talakan Nijeriya ya ci gaba da korafin so ake ya harbu da kwaronabairos, shi ya sa aka tilasta masa zuwa shiga cunkoson neman lambar shaidar dan kasa a wannan lokaci, maimakon a bari sai bayan cutar ta lafa, kamar yadda aka rufe makarantun boko da na Islamiyya.

4. Kwamitin kula da dakile yaduwar kwaronabairos na shugaban kasa, ya ce lallai yadda cutar kwaronabairos ke yaduwa babu kama hannun yaro a kasar nan, a ‘yan kwanakin nan, babu mamaki a yi kulle karo na biyu.

5. A yanzun haka akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1,565 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 807
Abuja 236
Kaduna 79
Oyo 57
Filato 47
Ribas 37
Katsina 35
Edo 30
Sakkwato 30
Delta 26
Kabbi 23
Ondo 20
Inugu 18
Abiya 17
Ogun 17
Binuwai 16
Bayelsa 15
Bauci 14
Neja 13
Kano 10
Barno 6
Imo 5
Ekiti 4
Oshun 2
Jigawa 1

Jimillar da suka harbu 95,934.
Jimillar da suka warke 77,982
Jimillar da ke jinya 16,622
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,330

6. Wani jami’i na hukumar kula da lafiya matakin farko NPHCDA, ya kawo shawarar idan an shigo da alluran rigakafin kwaronabairos kasar nan, a soma yi wa Shugaban Kasa Buhari da Mataimakinsa Osinbanjo, a gaban jama’a kai tsaye ta rediyo da talabijin, kowa ya ji ya gani, sannan a yi wa sauran jama’a, don kawar da shakku da zargin da ake yi wa allurar.

7. Hukumar kwastam ta ce a shekarar 2020 ta tara kudaden shiga har naira tiriliyan daya da rabi. Ta ma bude kan iyakar Illela ta jihar Sakkwato.

8. Malaman jami’a na cewa babu mamaki makon farko na watan gobe, su janye, janye yajin aikin da suka yi, yara su ci gaba da zaman dirshan a gida sai kuma yadda hali ya yi.

9. GwamnatinTarayya ta ce za ta ranci naira biliyan dari takwas da casa’in da biyar, daga asusun ajiya na jama’a da ke bankuna, da mai su ya dade bai taba ba, da ake kira DORMANT ACCOUNTS, da kuma ribar hannun jari wato DIVIDENDS da masu su suka dade ba su karba ba, don gudanar da wasu ayyuka da ake matukar bukata.

10. Hukumar EFCC ta ce ta lura ana saye da sayar da lambar shaidar dan kasa, ta ce to wallahi duk wanda ta yi ram da shi yana wannan sana’a za ta hukunta shi.

11. Kotu a jihar Kaduna ta sa ranar 25 ga watan nan don ci gaba da shari’ar zargin sayar da filin da ke harabar asibitin ido na kasa wato aisanta.

12. Wasu ‘yan bindiga da kidinafin, sun kashe mutum hudu a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, suka yi kidinafin wasu yawanci mata, da ji wa da dama rauni, sai dai jami’an tsaro da suka kai dauki sun ceto dukkan wadanda aka yi kidinafin

13. A Gaidam ta jihar Yobe, ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka je farautar kayan abinci da magunguna, da taba tsiyar da aka san bature da yinta a ranar da za shi gida.

14. A jihar Katsina, Gwamna Masari ya ce jami’an tsaro sun ceto mutum 104 da aka yi kidinafin a Safana, da Faskari, da Dan Musa, da Jibiya, da Batsari.

15. Sojoji sun ce sun kai farmaki sabon matsugunin Boko Haram da ke jihar Barno.

16. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari tun lokacin yakin neman zabe.

17. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

18. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, don duba shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis. A kuma leka jaridar Muryar ‘Yanci ta rediyo da talabijin na Libati.

Mu yi Juma’a lafiya.

Af! Limamai da za su hau mumbari yau kada ku manta da addu’ar Allah Ya mana maganin abubuwan da suka dame mu a wannan zamani. Ba laifi idan an hada da alkunut.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply