Home Labarai Taskar Guibi: 08.05.2020

Taskar Guibi: 08.05.2020

372
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha biyar ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S A.W. Daidai da talatin da takwas ga watan Afrilu, wasu kuma takwas ga watan Mayu, shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Ma’aikatan kwalejojin ilimi da na kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya da suka amince suka shiga tsarin IPPIS, na nan suna ci gaba da gunagunin yau takwas ga watan Mayu, talatin ga watan Afrilu, azumi ya kai goma sha biyar, ba dilin-dilin babu dalilinsa. Ariyas ma ya haura shekara ba a biya ba. Haka nan su ma malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya da suka bijirewa shiga tsarin na IPPIS, har yanzun suna watan Fabrairu bai kare ba, ballantana su shiga Maris, su shiga Afrilu, su shiga Mayu. Wato watansu na hudu ke nan babu dilin-dilin babu dalilinsa duk da tun 23 ga watan jiya, Baba Buhari ya ce a hanzarta biyan dukkan ma’aikata albashinsu. Ga wani can yana cewa Malam Guibi Baba Buhari fa bai san an kai yau ba a bi umarninsa ba.

2. Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce, bangaren nasu ya tabka asara ta naira biliyan ashirin da hudu sakamakon hana sauka da tashin jiragen sama saboda kwaronabairos.

3. Yau ake sa ran kwaso ‘yan Nijeriya da ke Ingila zuwa gida Nijeriya, sai dai za a biya da su Legas, amma a Abuja za a sauke su, ba kamar wadanda aka kwaso daga Dubai shekaranjiya da aka sauke su a Legas ba.

4. An bukaci kowacce jiha ta samar da waje/wuri mai gadaje dari uku don masu jinyar kwaronabairos.

5. Babbar kotun tarayya ta ci gwamnati tarayya tarar naira miliyan daya saboda ‘yan sanda sun tauye hakkin Sowore da mutanensa na ‘yancin yin zanga-zanga ta lumana da suke da shi a matsayinsu na ‘yan kasa.

6. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce akwai akalla ma’aikatan lafiya guda dubu daya da suka harbu da cutar kwaronabairos a Afirka.

7. Gwamnatin Tarayya ta soke duk wani haraji na fito da na tamanin kaya ga dukkan kayayyakin da za a shigo da su da suka jibanci yaki da kwaronabairos na tsawon wata shida daga daya ga wannan watan da muke ciki.

8. Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa NBC ta ce an yafe wa gidajen kudin da suka saba biya, na wata biyu saboda lalurar da ake ciki ta kwaronabairos.

9. Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta gargadi ‘yan sanda cewa tilasta aiki da dokar kulle ba lasisi ne na tauye hakkin bil’Adama ba. Shi kuma shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya gargadi masu karya dokar kulle su daina yi wa ‘yan sanda barazana.

10. An rage farashin man fetur zuwa naira dari da takwas kowacce lita a daffo. Na sha man jiya a A.A. Rano na wajen Kasuwar Bacci, Kaduna, na ga kowacce lita ta sauko naira dari da ashirin.

11. Kotunan-tafi-da-gidanka da aka kafa a jihar Kaduna sun ci mutum dari uku da goma sha daya da suka karya dokar kulle tara.

12. Gwamnatin Tarayya ta ce za ta soma ciyar da dalibai da ke gida.

13. Wasu sun harbe fasto da matarsa da diyoyinsa a jihar Filato.

14. A jihar Binuwai an harbi wani da matarsa.

15. Sojojin Nijeriya sun ce daga watan Maris na shekarar nan, zuwa wannan watan na Mayu, sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram dari uku da arba’in da uku, da ‘yan bindiga dari da hamsin da uku, suka ceto mutum goma sha takwas, suka kama kidinafas goma sha uku, suka kama mutum goma sha shida ‘yan rahoto ko masu tsegunta wa mahara. Sojojin sun ce sun kai hari inda ‘yan ISWAP suke a kusa da tafkin Cadi.

16. Za a ci gaba da ruguntsumi na bukukuwan aure da suna da sauran hada-hada a kasar Itali/Italiya bayan ta yi fama da mace-mace na tsawon wata biyu sakamakon kwaronabairos.

17. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, sabbi da suka harbu da kwaronabairos, su 381 ne a jihohi kamar haka:

Legas 183
Kano 55
Jigawa 44
Zamfara 19
Bauci 19
Katsina 11
Barno 9
Kwara 8
Kaduna 7
Gwambe 6
Ogun 5
Sakkwato 5
Oyo 3
Ribas 3
Neja 2
Akwa Ibom 1
Inugu 1
Filato 1

Da ke nuna zuwa jiya da daddare mutum 3,526 ya harbu a jihohi kamar haka:

Legas 1491
Kano 482
Abuja 316
Barno 125
Gwambe 109
Katsina 106
Bauci 102
Ogun 100
Kaduna 92
Sakkwato 89
Jigawa 83
Edo 65
Zamfara 65
Oyo 55
Oshun 37
Kwara 24
Kabbi 18
Akwa Ibom 17
Delta 17
Ribas 17
Adamawa 15
Taraba 15
Ondo 13
Yobe 13
Ekiti 12
Nasarawa 11
Inugu 9
Neja 6
Bayelsa 5
Ebonyi 5
Filato 5
Abiya 2
Binuwai 2
Imo 2
Anambra 1

Jama’a ni fa ba na ganin jihar Kogi ne kuma ban ji ana ta mutuwa a jihar ba? Ko ita ba a kasar nan take ba ne?

A yanzun mutum 3,526 ya harbu, 601 suka warke, 107 suka riga mu gidan gaskiya, saura 2,818 ke jinya.

Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito da safiyar nan, a wuraren sayar da ita, da kuma ta intanet don karanta labarun da na bayar ta dandalina na soshiyal midiya, daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis. Haka nan a lalubi Taskar Guibi da ke jaridar kamfanin sadarwa na DCL a intanet, a kuma nemi jaridar Muryar ‘Yanci ta Liberty/Libati rediyo da talabjin a intanet, a kuma lalubi dandalin labaru na KAINUWA a intanet, da sauran dinbin dandali daban-daban na wasaf da fesbuk, har da na Matasa A Yau, da gidajen rediyo da talabjin da ke daukar labarun nawa don karanta su ko saurarinsu. Ba zan mance wani tsohon dalibina na larabci Mu’az Bashir da shi ma kusan a kullum sai ya ya yi shiyarin labarun, haka nan Bello Falama da sauransu. Duk ina godiya kuma in Allah Ya yarda mun kusa bude GUIBI RADIO.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply