Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 09.06.2020

Taskar Guibi: 09.06.2020

145
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha bakwai ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Yunin shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Babban Hafsan Hafsoshin Mayakan Kasa na Kasar nan Buratai, ya je Fadar Shugaban Kasa Ya yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karin haske a kan inda aka kwana wajen yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan tsagera da ‘yan bindiga, har ya ce sun kashe dubu daya da dari hudu, suka kama da dama, har da masu tsegunta musu ko ‘yan rahotonsu.

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da sunan Dangbam a matsayin shugaban kotun daukaka kara.

3. Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Yaduwar Miyagun Cututtuka, da takwarorin kwamitin da ke jihohi, sun soma zuwa gaban kwamitin majalisar dokoki ta kasa, don bayyana yadda suka kashe kudaden gudunmawa da aka ba su don yaki da cutar kwaronabairos. Wata majiya na cewa Kano ta kasa bayyana yadda ta yi da nata kudin.
Ana kuma korafin Babban Akanta na Kasa yana ta kin amsa gayyata.

4. Gwamnan Kogi Yahya Bello ya ce yana nan a kan bakarsa ta cewa karya hukumar yaki da cututtuka ta kasa NCDC ta yi wa jiharsa cewa akwai mutum na farko da ya harbu da kwaronabairos a jiharsa. Ya ce binciken da ya yi ya gano har zuwa yau ba wanda ya taba harbuwa da cutar a jihar tasa. Ita kuwa hukumar ta NCDC ta ce gwajinta ya sa ta gano akwai wanda ya harbu a jihar.

5. Likitoci har da masu duba masu jinyar kwaronabairos da ke fadin kasar nan, za su soma yajin aiki a makon gobe, a korafe-korafensu har da likitocin jihar Kaduna da aka yankewa albashi ba da yardarsu ba.

6. Wadume da tsohon kyaftin din nan na soja sun ce atabau, ba su aikata laifin da ake tuhumarsu sun aikata ba, na kisan ‘yan sandan da suka kamo Wadume da sakinsa.

7. Gwamnatin jihar Nasarawa ta kori Sakataren Gwamnatin jihar Saboda wasu kudi na ilimi naira biliyan daya.

8. Babban Bankin Nijeriya zai ba da tallafin kudi naira miliyan dari biyar da hamsin don bincike bangaren lafiya.

9. Kamfanin Mai Na Kasa NNPC, zai gina asibiti na naira biliyan daya a Kaduna.

10. Asabar da ta gabata da daddare kidinafas sun je Kwanar Farakwai da ke jihar Kaduna sun yi kidinafin wani, ga kuma mutum shida da suka je Gwanin Gora duk da ke jihar Kadunan da daddare suka yi kidinafin har da yara kanana.

11. Yau ake sa ran gwamnan jihar Kaduna zai yi jawabin inda aka kwana a kan kulle a jihar Kaduna. Da ma akwai walwala yau da gobe da jibi ta tara kayan abincin kulle.

12. Kidinafas sun tafi da shugaban kotun gargajiya na jihar Taraba.

13. Gwamnan jihar Abiya Ikpeazie ya harbu da kwaronabairos, ya ce ai ciwo ba mutuwa ba ne.

14. Tana kasa tana dabo a kan zaben-fid-da-gwani na wanda zai tsaya wa APC takarar gwamna a jihar Edo.

15. Kotu ta yi fatali da bukatar kada a ci gaba da bincikar tsohon sarkin Kano Sanusi na biyu a kan zargi ya yi ba daidai ba da Gandun Sarki na naira biliyan biyu.

16. Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da izinin bude kasuwanni.

17. Tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ya cika shekara ashirin da biyu da rasuwa.

18. Sanata Ndume ya kawo shawarar a yanke wa kowanne ma’aikaci albashi tunda ba aikin ake zuwa ba ana zaune a gida.

19. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da sauran sanatoci, sun je taya Sanata Uzor Kalu murnar sako shi, bayan daure shi da kotu ta yi a kan wata naira biliyan bakwai da ‘yan kai da ake zargin ya wawura. Har wasu ke cewa sanatocin suna taya shi murnar nasarar da ya samu a kan kudin Nijeriya da ya wawura.

20. Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Gwambe ya harbu da kwaronabairos.

21. Kamfanonin nemo wutar lantarki GENCOs sun soki batun soke sayar musu da lamuran lantarki gabadaya, suka ce suna bin kudin wuta har ta naira tiriliyan daya.

22. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wajen wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ta korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun wannan shekarar.

23. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbi da suka harbu da kwarona su 315 a jihohi kamar haka:

Legas 128
Abuja 34
Ribas 32
Edo 28
Oyo 22
Kaduna 20
Gwambe 13
Ogun 8
Filato 5
Delta 7
Kwara 7
Kano 5
Bauci 4
Katsina 2

Kowacce jiha tana da alkalumma kamar haka:

Legas 5,895
Kano 1,004
Abuja 986
Edo 429
Katsina 397
Oyo 387
Ribas 364
Kaduna 363
Ogun 363
Barno 358
Bauci 295
Jigawa 283
Gwambe 230
Delta 155
Kwara 142
Sakkwato 129
Filato 120
Nasarawa 112
Ebonyi 103
Abiya 83
Zamfara 76
Imo 68
Yobe 52
Oshun 49
Akwa Ibom 45
Neja 44
Adamawa 42
Ondo 42
Kabbi 35
Bayelsa 30
Inugu 30
Anambra 29
Ekiti 29
Taraba 18
Binuwai 13
Kogi 3
Kuros Ribas 0

Wadanda suka harbu 12,801
wadanda suka warke 4040
wadanda suka riga mu gidan gaskiya 361
wadanda ke jinya 8,400

Mu wayi gari lafiya.

Af! An ce an ji shiru kwana biyu ban ce komai a kan matsalolin Kinkinau ba. To har kun tuna mun an ce mahaukaci ba ya jifa. Hanya ta gagara a Kinkinau. Asibitin Amina Namadi Sambo da ke zaman-zamansa aka yaye kwanonsa mai tsada aka sa mai arha, yau fiye da shekara uku an kashe asibitin. Sai ofishin kasteliya da ke bayan asibitin ake duba majinyata na dan wani lokaci. Ruwan fanfo suna dan kawowa a damunar nan kodayake an ce ba don Allah suke kawowa ba. Ruwan sama ne ya cika tukwanen nasu suke neman kai da shi. Sai wutar lantarki ita ma ba dan laifi ana samu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply