Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 09.09.2020

Taskar Guibi: 09.09.2020

353
0

Assalama alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shagaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna ba gudu ba ja da baya a janye tallafin da ake yi wa kudin man fetur. Daga yanzun kasuwa ce za ta iya kayyade farashin man da ‘yan Nijeriya ke saye.

2. An gano hukumomi da ma’aikatun gwamnati ba su zuba naira tiriliyan daya da ‘ya kai lalitar gwamnati ba.

3. An mayar wa wasu fulani shanunsu da suka haura hamsin da daya, da barayin shanu suka sato su daga jihar Taraba, aka kai su jihar Yobe.

4. Kidinafas a Kaduna, sun kashe dan sanda, da sibildifense da wani mutum guda, da aka yi kidinafin a Marabar Rido.

5. Sojoji sun kashe Akwaza da aka fi sani da MAKASHI a jihar Binuwai.

6. Daga makon gobe, sauran ma’aikatan lafiya da ba likitoci ba JOHESU za su soma yajin aiki na mako daya na gargadi.

7. A shekara goma sha biyar, an kashe naira tiriliyan goma da kusan rabi wajen tallafa wa man da talakan Nijeriya ke saye.

8. An kama wasu ‘yan Nijeriya hudu a kasar Filifin da laifin damfarar banki.

9. Kungiyar malaman jami’o’i ta yi kiran da a rage kudin mai da na lantarki da aka kara.

10. Malaman kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna jiran ariyas.

11. Wannan karon cutar kwaronabairos ta nunfasa saboda akwai mutum 296 sabbin harbuwa a jihohi da alkalumai kamar haka:

Filato 183
Legas 33
Abuja 25
Ogun 16
Oyo 7
Ekiti 6
Kwara 5
Ondo 5
Anambara 3
Imo 3
Nasarawa 3
Ribas 2
Gwambe 2
Edo 1
Akwa Ibom 1

Jimillar da suka harbu 55,456
Jimillar da suka warke 43,334
Jimillar da ke jinya 11,055
Jimillar da suka rigamu gidan gaskiya 1,067

12. Mutanen kauyen Guibi ta karamar hukumar Kudan da ke jihar Kaduna na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ba taki ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

13. Wata majiya na cewa likitocin da suka fara yajin aiki, sun janye yajin aikin.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Addu’ata kullum ita ce Allah Ya mana katangar karfe da musamman munafiki, kuna tare ba abin da ba ka masa amma munafunci da cin diddigenka, su ne babbar sana’arsa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply