Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 10.01.2021

Taskar Guibi: 10.01.2021

210
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin da biyar ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1,585 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 573
Abuja 182
Filato 162
Gwambe 81
Oyo 75
Ribas 68
Sakkwato 58
Ondo 55
Ogun 42
Nasarawa 40
Akwa Ibom 36
Edo 31
Kaduna 27
Anambara 22
Delta 19
Kano 17
Oshun 17
Ebonyi 16
Katsina 14
Neja 14
Bayelsa 9
Ekiti 8
Barno 7
Jigawa 5
Abiya 4
Bauci 3.

Jimillar da suka harbu 99,063
Jimillar da suka warke 79,417
Jimillar da ke jinya 18,296
Jimillar da suka warke 1,350

2. Kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna ta harbu da kwaronabairos.

3. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawarin zai gyara musu idan sun zabe shi. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.

4. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

5. Malaman jami’a na ci gaba da korafin Gwamnatin Tarayya, ta soma sa kafa tana fatali da yarjejeniyar da suka kulla da ita, har suka janye yajin aiki. Da korafin idan gwmnatin ta ci gaba sa shure yarjejeniyar, to za su koma yajin aiki a farkon watan gobe na Fabrairu.

6. Kotu ta yi fatali da karar da APC ta kai Gwamna Obaseki na jihar Edo kotu, cewa takardar shaidar karatunsa ta jami’a jabu ce.

7. Hukumar ‘yan sanda ta Nijeriya, ta bullo da wata sabuwar manhajar gano inda ake aikata laifi cikin sauki, da daukar mataki cikin hanzari don kyautata tsaro a kasar ban.

8. Hukumar Sojan Nijeriya ta kaddamar da rawar soja mai suna TURA TA KAI BANGO, don gamawa da ‘yan kungiyar Boko Haram da su ISWAP da dangoginsu.

9. Hukumar Kula da Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC, ta ce nan gaba kadan, sai kana da lambar shaidar dan kasa sannan za a iya maka tarkardun mota da lasisi ko sabunta su.

10. Kamfanonin sadarwa ta waya, sun ce daga yanzun sai kana da lambar shaidar dan kasa za su iya maye maka gurbin layinka da ya bace, ko aka sace ko ya lalace.

11. Mamallaka Dandalin Sadarwa ta Twita, sun dakatar da Donald Trump daga amfani da dandalin nasu, saboda zargin yana amfani da dadandalin wajen tunzura jama’a.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina nan ina shirin horar da ma’aikatan gidan rediyon jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya. Kada a manta na horar da wadannan:

i. NTA
ii.FRCN
iii.KSMC
iv. NUJ
v. NewAge Network
vi. Kaduna Media Academy
vii NAGARTA
viii FREEDOM
ix. LIBERTY
x.ALHERI RADIO
xi. KASU F.M.
xii. Mass Communication Students, Kaduna Polytechnic.

Sai A.B.U. FM da ke biye.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply