Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 10.06.2020

Taskar Guibi: 10.06.2020

159
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha takwas ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da rabon kayan aikin gona na damunar bana a jihar Kaduna, inda gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ce zai kawar da ‘yan bindigan da suka addabi jihar Kaduna don manoma su ji dadin zuwa gona.

2. Hukumar Kula da Hada-hadar kasuwanci ta duniya WTO ta amince da sunan Okonja Iweala da shugaban kasa Buhari Buhari ya bayar.

3. Shugaban Majalisar Wakilai ya ba likitoci da ke shirin zuwa yajin aiki makon gobe hakuri, har ma gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a hanzarta biyan likitocin wani alawus da suka yi korafi a kai HAZARD ALLOWANCE na watan Afrilu da na Mayu.

4. Limamin da ake zargin shi ne na farkon harbuwa da kwaronabairos a jihar Kogi, har ya kai ga gwamnan jihar Yahya Bello tilasta kulle a Kabba-Bunu, ya fito fili ya ce kage aka masa bai harbu da cutar ba.

5. A jihar Neja za a bude kasuwanni da bankuna da hadar-hadar sufuri.

6. A Kaduna an yi ruwan sama wanda ke gauraye da tabo, da daddare kuma aka yi ruwan shinge.

7. A jihar Yobe ruwa da iska da tsawa sun yi sanadiyyar mutuwar mutum shida har da mai juna biyu.

8. A jihar Barno ruwa da iska sun yi gyara a wani sansanin ‘yan gudun hijira.

9. Mutum goma sha bakwai aka kashe a jihar Taraba, a wani rikici na Munci da Jukunawa.

10. Al’umar ‘Yantumaki da ke jihar Katsina, sun yi zanga-zanga saboda ci gaba da kashe su da sace su da kidinafas ke yi. An ma ce al’umomi da dama na kananan hukumomin jihar ta Katsina na ta gudun hijira saboda an zo zamanin da zaman jihar Katsina ya gagara.

11. Sanata Uzor Kalu ya halarci zaman Majalisarsa ta Dattawa, bayan sako shi daga gidan kaso.

12. Sojoji sun ce sun lalata wuraren ‘yan bindiga da kashe su da dama a Dajin Kwayanbana da ke jihar Zamfara.

13. ‘Yan kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai zafafan hare-hare a jihar Barno har da jikkata sojoji.

14. Majalisar Wakilai ta nemi shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya binciki harin da ‘yan fashi suka kai banki a jihar Kogi.

15. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata biyu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

16. Ana batun ba da belin dan sanda Derek da ya kashe George Floyd a Amurka zai biya kudin belinsa dala miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin, ana kuma tunanin rusa sashin ‘yan sanda na Amurka saboda wannan kasassaba da ‘yan sandan suka yi. Jiya aka bisne George.

17. Shugaban kasar Burundi Nkurumziza mai shekara 55 a duniya ya riga mu gida gaskiya sakamakon bugun zuciya.

18. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin wadanda suka harbu da kwaronabairos su 663 a jihohi kamar haka:

Legas 170
Ogun 108
Bauci 69
Ebonyi 49
Edo 33
Ribas 30
Abuja 26
Jigawa 26
Delta 20
Anambra 17
Gwambe 16
Kano 16
Imo 15
Abiya 14
Barno 11
Oyo 11
Filato 8
Kabbi 6
Kaduna 6
Ondo 4
Neja 2
Katsina 2
Oshun 2
Ekiti 1
Kwara 1
Nasarawa 1

Da ke nuna zuwa jiya da daddare kowacce jiha tana da:

Legas 6,065
Kano 1,020
Abuja 1,012
Ogun 471
Edo 462
Katsina 399
Oyo 398
Ribas 394
Kaduna 369
Barno 364
Jigawa 309
Gwambe 246
Delta 176
Ebonyi 152
Kwara 143
Sakkwato 129
Filato 128
Nasarawa 113
Abiya 97
Imo 83
Zamfara 76
Yobe 52
Oshun 50
Anambra 46
Neja 46
Ondo 46
Akwa Ibom 46
Adamawa 42
Kabbi 41
Bayelsa 30
Ekiti 30
Inugu 30
Taraba 18
Binuwai 13
Kogi 3**
Kuros Ribas 0

Na sa wa Kogi taurari ne saboda Gwamna Yahya Bello ya ce a saninsa kage aka yi wa jiharsa aka ce mutum uku sun harbu. Ya ce a iya saninsa babu kowa da ya harbu da cutar a jihar tasa.

Jimillar wadanda suka harbu 13,464
Jimillar wadanda suka warke 4,206
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 365
Sai wadanda ke jiny, 8,893.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cire dokarta ta tilasta kulle da rana dayani, sai daga karfe takwas na dare zuwa karfe biyar na asubah daga yau. Sallah a jam’i a masallaci daga ta juma’a sai ta wata juma’ar, haka nan coci daga lahadi sai wata lahadin. Ba kasuwa ba makaranta tukuna. Ma’aikata za su je aiki daga karfe tara na safe zuwa uku na rana. Akwai zirga-zirga ko’ina kuma an haramta duk wani shinge na jami’an tsaro, sai dai ba a yarda a tsallaka wata jiha ba. Amna ko’ina mutum ya ga dama zai je a cikin jihar Kaduna.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply