Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 10.11.2020

Taskar Guibi: 10.11.2020

377
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da hudu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

1. Yau goma ga watan Nuwamba, wato arba’in da daya ga watan Oktoba ga yawancin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya bangaren ilimi. Bari in muku gwari-gwari. Har yau yawancin ma’aikata, misali na kwalejin foliteknik ta Kaduna ba su ga albashin watan jiya ba. Kuma sun kusan shekara ko ma fiye da shiga tsarin IPPIS. Haka ma albashin watan Satumba, sai da watan Oktoba ya raba biyu, sannan suka ga dilin-dilin na watan Satumba. Sannan suna korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi. Ariyas din da aka dede da biyan sauran ma’aikata da ba na bangaren ilimi ba. Laifin da suke dorawa ga tsarin IPPIS.

2. Kugiyar malaman jami’o’i ta ce ba fa laifinta ba ne dalibai ke ci gaba da zaman kashe wando a gida. Sun ce laifin Gwamnatin Tarayya ne. Ita ke nuna ba ilimin ne a gabanta ba. Wata takwas ke nan ba a biyan malaman albashi.

3. Kungiyar Ma’aikatan Fetur da Gas, PENGASSAN ta soma yajin aiki bayan karewar wa’adin da ta ba Gwamnatin Tarayya. Da ke nuna idan gwamnatin ba ta yi wani abu cikin hanzari ba, za a shiga wahalar mai da gas. Sun ce suna bin albashi da sauransu.

4. Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Farfesa Yakubu ya sauka daga mukaminsa ya mika wa Iya Bayis Mashal Ahmed Mu’azu mai ritaya riko, saboda kamar yadda Farfesan ya bayyana, bai kamata ya wuce jiya yana kan mukamin nasa ba, saboda a jiyan wa’adinsa ya kare. Kuma ba a kammala batun sake nada shi da Shugaban Kasa ya yi ba.

5. Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya harbu da kwaronabairos.

6. A duniya bakidaya mutum miliyan hamsin ya harbu da kwaronabairos. A Nijeriya akwai sabbin harbuwa 94 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 50
Abua 24
Kwara 9
Edo 4
Kaduna 3
Ondo 2
Filato 2

Jimillar da suka harbu 64,184
Jimillar da suka warke 60,069
Jimillar da ke jinya 2,967
Jimillar da suka riga ni gidan gaskiya 1,158

7. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce nan gaba kadan za a yi dokar da za ta tabbatar da karba-karba, na sarauta, a musamman gidajen da suka gaji saurauta, kamar yadda yake a Masarautar Zazzau.

8. A jiya aka rantsar da Sarkin Zazzau na goma sha tara, Ahmad Nuhu Bamalli da mika masa Sandar Girma. A wadanda suka halarci bikin a Zariya, har da gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu da na jihar Filato Lalong.

9. Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin wani kwamisha na jihar Zamfara hari, har suka kashe daya daga cikin direbobinsa.

10. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau ta gagara. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi. Har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

11. Gwamnati ta bayyana cewa babu wani albashi na musamman da aka tsara wa dakarun SWAT da suka maye gurbin SARS.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Pfizer na Amurka, da hadin gwiwar Bio-Tech na Jamus, ya yi nasarar samar da rigakafin cutar kwaronabairos. Sun gwada shi a kasashe shida, a mutum fiye da dubu arba’in da uku, kuma an ga ingancinsa cif-cif. Har Shugaban Kasa Muhamadu Buhari ya nuna farin cikinsa, da kuma rokon a samu EQUITABLE DISTRIBUTION na VACCINE din.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply