Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 11.01.2021

Taskar Guibi: 11.01.2021

254
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Litinin, ashirin da bakwai ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Janairu, 2021.

1. Yau ma’aikatan Hukumar Rajistar ‘Yan kasa za su koma bakin aiki don ci gaba, da yi wa ‘yan kasa rajista da ba su lambar shaidar dan kasa. In ba a manta ba, sun yi wani yajin aiki na gargadi a makon jiya, saboda korafin in suka ci gaba da yi wa jama’a rajista, to za su harbu da kwaronabairos, da kuma sauran korafe-korafensu.

2. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1,024 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 653
Filato 63
Binuwai 48
Zamfara 45
Abuja 42
Ribas 27
Ondo 26
Adamawa 26
Kaduna 22
Edo 18
Ogun 16
Imo 12
Kano 9
Yobe 6
Ekiti 5
Jigawa 4
Oshun 2

Jimillar da suka harbu 100,086
Jimillar da suka warke 80,000
Jimillar da ke jinya 18,729
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,358

3. Sojoji sun ce a hanyar Bauci zuwa Maiduguri sun kashe ‘yan bindiga ashirin.

4. Sojoji sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga hamsin, da kwato shanu dari biyu da saba’in da biyar a jihar Zamfara da ta Katsina.

5. ‘Yan sanda sun bukaci ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara, ko su ajiye makamai su tuba, ko su yaba wa aya zaki kwanan nan.

6. An ja hankalin jami’an tsaro da ke cewa sun kashe ‘yan bindiga da kwato shanu masu yawa, su dinga iya bambace ainihin makiyaya da ke yawo suna kiwo da shanunsu, da kuma barayin shanu.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

8. Da yake yau Litinin, mutanen jihar Kaduna musamman cikin garin Kaduna, kada a manta da takunkumi, domin in aka kama mutum bai sa ba, akwai tara ta naira dubu ashirin, in mutum ya ma yi sa’a bai ci na jaki ba.

9. George Obiazor aka zaba shugaban kungiyar Inyamurai Ndigbo Ohaneze, da rinjayen kuri’a dari uku da hudu.

10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Akwai gidajen rediyo da talabijin da ke fassara jaridun turancin Ingilishi kai tsaye da safe. Gaskiya yawancin masu yin fassarar kai tsaye, KASSARA suke yi ba FASSARA ba. Kuma wai bayan sun gama kassara fassarar labarun jaridun, sai su bude layi su ce jama’a su kira su tofa albarkacin bakinsu a kan labarun da suka kassaro daga jaridun. A nemi wadanda suka iya fassara kai tsaye, akwai su a cikin gidajen rediyo da talabijin da nake korafi a kan su, in ba su da kudin dauko wasu daga waje, ko shirya tarukan bita ko horaswa ta cikin gida.Wannan kassara da suke yi na kassara mutuncin gidajen rediyonsu da talabijin. Ko jiya da na ji wannan baharlatsar a wani gidan rediyo, sai da na kira shugabannin rediyon a waya, na ba su shawarar, su dinga tilasta wa masu fassara jaridun kai tsaye, suna fassara kalmomin da ke musu tsauri, a wata takarda a gefe a kan kowanne labari, in har ba su da lokacin zama, su yi fassarar da kyau a wata takarda, kafin su shiga shirin karanto wa jama’a kanun jaridun.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply