Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 11.02.2021

Taskar Guibi: 11.02.2021

120
0

Assalami Alaikum jama’a barkanmu da asubahin Alhamis, ashirin da takwas ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Fabrairu na shekarar 2021.

1. Jiya hukumar da ke kaso da raba alkaluman kwarona, ta raba wa jihohi kwarona 1,131 kamar haka:

Legas 297
Abuja 194
Kaduna 83
Kano 59
Oyo 58
Imo 52
Oshun 47
Folato 45
Edo 43
Akwa Ibom 42
Ribas 42
Ogun 29
Kwara 24
Binuwai 21
Nasarawa 16.
Ekiti 7
Bauci 6
Delta 6
Bayelsa 4
Sakkwato 2
Gwambe 1

Kason da aka bayar na wadanda suka harbu da kwarona zuwa yanzun, 142 578
Kason da aka ba wadanda aka ce sun warke 116,937
Kason da aka ba wadanda aka cr masu jinya ne 23,929
Kason da aka ba wadanda aka ce sun riga mu gidan gaskiya shi ne 1,702.

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Wakilai wasikar neman su amince da nadin da ya yi wa tsofaffin hafsoshin tsaron kasar nan, mukaman jakadu. Su kuma amince masa da sabbin da ya nada hafsoshin tsaron kasar nan.

3. A zaman Majalisar Dattawa na jiya, da na Majalisar Wakilai duk a jiyan, sun tabo batun rashin tsaro da ke ci gaba da addabar kasar nan.

4. Kungiyoyin kwadago sun nuna ba su yarda da yunkurin da Gwamnatin Tarayya ta yi na kara kudin man fetur ba.

5. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun ci gaba da barnar da suka saba yi, ta lalata manyan turakun wayoyin lantark da na wayoyin sadarwa a Maiduguri.

6. A Gaidam ta jihar Yobe ‘yan kungiyar Boko Haram sun je garin sun ci karensu ba babbaka son ransu, suka gama suka yi tafiyarsu.

7. Kotu ta ba da umarnin sakarwa asusun banki na jagororin gwagwarmayar kawo karshen ‘yan sandan SARS mara.

8. Hukumomin sojan Nijeriya, sun nada sabon daraktan yada labaru da hulda da jama’a na soja Birgediya Janar Yerima, don maye gurbin tsohon Birgediya Janar Sagir Musa da aka tura wajen horas da soja da ke Kwantagora.

9. Auwal Daudawa da ake zargin shi ne jagoran kidinafin ‘yan makarantar Kankara, ya tuba ya yi saranda a ahuwar da ake yi wa ire-irensa. Shi kuma tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Jibiya Haruna Musa da ake zargin yana alaka da kidinafas, an ci gaba da tsare.

10.Gangar danyen mai ta ci gaba da shanawa inda ta kai dala sittin da daya kowacce lita a kasuwar duniya.

11. A ranar 15 ga watan nan ne Cibiyar Hadahadar Kasuwanci ta Duniya WTO za ta sanar da Okonjo Iweala a matsayin shugabar cibiyar a hukumance.

12. An rada wa jami’ar jihar Bauci sunan Sa’adu Zungur.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da kwalejojin ilimi, da jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

14. Asusun Lamani na Duniya IMF ya ce tattalin arzikin Nijeriya na cikin wani mawuyacin hali.

15. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya ce idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.

Mu wayi gari kafiya.

Af! Allah Ka mana katangar karfe da kidinafas a duk inda muke Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply