Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 11.12.2020

Taskar Guibi: 11.12.2020

436
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da biyar ga watan Rabiul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Disamba na 2020.

1. Shugaban Majalisar Wakilai Femi, ya ce yana dakon shugaban kasa Muhammadu Bugari ya aika a hukumance, dalilan da suka sa bai samu cika alkawarin da ya yi na zai je Majalisar jiya ba.

2. An ci gaba da shari’ar Maina ke nan jiya, sai ya yanke jiki ya fadi, kamar yadda na ji BBC Hausa suka fassara faduwar tasa da ya yi zama irin na ‘yan bori. Shi kuwa dansa Faisal da ake zargin ya cika rigarsa da iska, a tasa shari’ar, shi ma an damko shi.

3. Shugaban Kwamitin Dakile Yaduwar Kwaronabairos Boss Mustapha, ya ce goguwar kwaronabairos ta sake yunkurowa tana nausawa karo na biyu a kasar nan, idan aka yi la’akari da yawan wadanda ke ta harbuwa a ‘yan kwanakin nan.

4. Buratai ya dakatar da wani taro nasa, saboda wani dakare na soja, Manjo Janar John, shugaban rundunar soja ta Fatakwal da ke halartar taron a Abuja, ya harbu ranar Talata, ya riga mu gidan gaskiya jiya. Har Buratai ya umarci dakarun soja da suka halarci taron kowa ya killace kansa.

5. A jihar KadunaGwamna El-Rufai ya ce kwaronabairos na karuwa da babu mamaki a sake tilasta kulle. Sannan a ta daya bangaren an kammala rusa gidajen da ke aisanta da ke Mahuta. Sai kuma kotu da ta umarci kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya binciki masu zaben sarki a masarautar Zazzau da ya tsahirta.

6. Majalisar Dattawa ta nemi Shugaban Kasa ya mayar da Dafta Nasiru Argungu kujerarsa ta shugaban hukumar samar da aikin ta kasa NDE, da bincikar abin da ya hada shi da Keyamo har ya cire shi, ya nada Abubakar Nuhu Fikpo riko.

7. ‘Yan sanda sun kamo mutum biyu, daga cikin kidinafas goma sha biyar da suka yi kidinafin Ba Amurken nan da sojojin kundunbala na Amurka suka shigo suka kwace shi da karfi da yaji suka tafi da abinsu Amurka.

8. Wasu da ake zargin ‘yan tada kayar baya ne, sun kashe sojojin Nijeriya goma a jihar Borno, kamar yadda wata majiya ta tabbatar. A cewar majiyar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Alagarno da ke karamar hukumar Daboa, saidai hukumomi ba su yi Karin bayani kan batun ba. Majiyar ya ce mayakan ISWAP sun farwa sojojin da ke kusa da hanyar Alagarno, inda suka kashe sojojin goma tare da sace daya. A lokacin harin, ‘yan ta’addan sun sace tankokin yaki hudu, da kayan yakin rundunar sojojin kamar yadda majiyar, ya shaida wa Daily Trust.

9. A jihar Neja kidinadas sun yi kidinafin wani mai gari, da shugaban matasan APC da kuma wasu.

10. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Pantami, ya ce daga watan Janairu na shekarar nan zuwa yanzun, gwamnati ta rage kudin damar watayawa ta intanet wato DATA da kashi hamsin.

11. Malaman jami’a sun ce Gwamnatin Tarayya suke jira ta motsa, sai su ma su motsa yara su koma makaranta.

12. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na jami’o’i da na kwalejojin ilimi duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekarar da ke shirin kankama, sun cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

13. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na godo ga shugaban karamar hukumar Kudan mai shirin barin gado, Jaja, ya daure ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari tun lokacin yakin neman zabe. Alkawarin da shi ya sa suka zabe shi, ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

14. A nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fito an jima da safe, don duba shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku, daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis.

15. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 675 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 183
Legas 128
Kaduna 85
Kwara 57
Katsina 50
Filato 42
Ribas 39
Kano 33
Ondo 21
Ogun 17
Bauci 10
Sakkwato 5
Edo 2
Ekiti 1
Bayelsa 1
Delta 1
Jimillar da suka harbu 71,344
Jimillar da suka warke 65,474
Jimillar da ke jinya 4,680
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,190

Mu wayi gari lafiya, mu yi Juma’a lafiya.

Af! A ranar 8 ga watan Disamba, na 2015, shekara biyar ke nan da doriyar kwana uku, na yi wannan rubutun a kan VIO na Kaduna:

“Jiya za ni aiki na gitta ta ma’aikatar ayyuka ta jihar Kaduna wato ofishin VIO jami’an duba lafiyar ababen hawa, sai na lura gilasan tagogin wajen a farfashe. Na tambaya me ya auku a nan kamar an yi yakin Badar? Aka ce VIO ne suka bi wani mai mota a guje ya fada wajen masu cuwa-cuwar mai wuta ta kama har wani ya mutu. shi ne mutane suka bi VIO har ofis suka mayar da martani. To dama akwai korafe-korafe a kan VIO a jihar Kaduna don shi kansa Gwamna El-rufai ya ce cin hanci da rashawa da VIO ke yi ke hana gwamnatin jiha samun kudaden shiga. VIO ke buga takardun bogi su dinga sayarwa da masu ababen hawa. Ga su sun iya halin dabbobi da ‘yan tasha Idan suka tare hanya. Yawancinsu kananan ma’aikata ne sai ka ga suna kece-raini da manyan motoci masu tsada da gidaje masu tsada da mata masu tsada duk da kudin rashawa da cin hanci. Da wuya ka yi laifi ROAD SAFETY su bi ka a guje saboda kiyaye hadura. Amma VIO sai su bi ka a guje saboda kwandalar da za ka ba su. Gaskiya akwai gyara kam a aikin VIO a Kaduna”

Hmmm!

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply