Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 12.01.2021

Taskar Guibi: 12.01.2021

208
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da takwas ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1244 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 774
Abuja 125
Filato 102
Anambara 47
Ondo 46
Ribas 27
Edo 18
Kaduna 16
Gwambe 16
Bauci 11
Kano 11
Nasarawa 10
Akwa Ibom 7
Sakkwato 7
Barno 5
Ekiti 4
Zamfara 2

Jimillar da suka harbu 101,331
Jimillar da suka warke 80,491
Jimillar da ke jinya 19,479
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,361

2. Da farko karamin ministan lafiya Mamora ya ce saboda yadda kwaronabairos ke ta kara yaduwa, babu mamaki a dakatar da rajistar ‘yan kasa da ba su lambar shaida. Daga baya ya ce shugaban kasa ne kadai zai iya dakatarwar.

3. Jiya ma’aikatan da ke aikin rajistar shaidar dan kasa suka ci gaba da aiki bayan janye yajin aikin da suka soma, a kan korafin suna iya harbuwa da kwarona da sauran korafe-korafensu. Sai dai sun ce nan da mako uku idan suka ji shiru bangaren gwamnati, za su ci gaba da yajin aiki.

4. Ana zargin akwai baraka a gwamnatin Baba Buhari. Boss Mustapha da kwamitinsa na dakile yaduwar kwaronabairos na ta fitar da ka’idojin kaucewa yadawa ko daukar cutar, ana zargin ministan sadarwa Pantami da rushe ka’idojin ta hanyar nacewa dole sai an yi rajistar dan kasa, a wannan lokaci. Inda jama’a ke cincirindon da Boss ya hana.

5. Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar fasa bude jami’o’i ranar 18 ga watan nan saboda yadda kwaronabairos ke ci gaba da hauhawa.

6. A yau ma’aikatan jami’o’i da aikinsu ba na koyarwa ba ne NASU, da manyan ma’aikatan jami’o’in SSANU, za su soma wani yajin aiki na gargadi na yini uku.

7. Kungiyar Malaman jami’o’i ta ce gaskiya bai kamata a bude jami’o’i 18 ga wata ba, saboda ba a yi wadataccen tsarin kare dalibai da malamai daga kwaronabairos ba.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Hukumar ‘yan sandan ciki DSS ta ankarar cewa akwai wasu da ke shirin kunna wutar rikicin addini a wasu jihohin kasar nan.

10. Kotu ta ba da belin Sowore a naira miliyan ashirin da wasu mutum biyu da za su tsaya masa.

11. An yi gobara a shalkwatar imigireshan da ke Abuja.

12. ‘Yan bindiga sun sa wa al’umomin jihar Neja harajin naira miliyan biyar duk wata in suna so su zauna lafiya.

13. GwamnatinTarayya ta sa hannu a kan aikin reliwe daga Kano zuwa Maradi, da zai ci dala biliyan biyu ba wasu ‘yan canji (1.9).

14. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo ga shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya daukar musu a lokacin yakin neman zabe, na in sun zabe shi zai gyara musu gada. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kamar yadda na yi bayani kwanakin baya, wasu na zargin hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa na ba ni kudin data da nake sa alkaluman wadanda suke harbuwa da kwarona kullum. Gaskiya ba wanda ya taba ba ni ko taro. Amma in akwai wanda zai mun hanya a dinga raba makudan kudin da ni ba matsala.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply