Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 12.11.2020

Taskar Guibi: 12.11.2020

363
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahim Alhamis, ashirin da shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammas S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Nuwamba na shekarar 2020.

1. Ana cikin makokin rasuwar Dan Iyan Zazzau Hakimin Kabala Alhaji Yusuf Ladan, sai kuma ga rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Abdullkadir Balarabe Musa. Kamar ‘yan soshiyal midiya sun san ya kusan rasuwa, suka dinga sa dinbin ayyukan da ya yi cikin dan lokacin da ya yi yana gwamnan jihar Kaduna daga watan Oktoba na shekarar 1979 zuwa watan Yuni na shekarar 1981. An haife shi a 1936 da ke nuna ya rasu yana da shekara tamanin da hudu a duniya. Ya rasu ya bar iyali da manyan ‘ya’ya maza da mata. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aiko da gaisuwar ta’aziyyarsa. Tsofaffin gwamnonin jihar Kaduna Sanata Makarfi, da Ramalan Yero na cikin dinbin wadanda suka masa Sallah a masallacin Sarkin Musulmi Bello.
Allah Ya jikan musulmi da suka riga mu gaskiya, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.

2. An mike gadan-gadan ana wayar wa da masu korafin sai an cire rubutun ajami (‘Gagara mai shi’ in ji malamina marigayi Rabiu Zarruk da shi ya koya mana AJAMI a karatun digiri na farko a ABU a 1988/1989) daga jikin kudin Nijeriya. Masu korafin sai an cire AJAMIN sun dauka Larabci ne ko kalma ce ta Alkur’ani mai girma, wato a tunaninsu an musulantar da kudin Nijeriya ke nan. To ba larabci ba ne, kuma da za a dauko balarabe a ce ya karanta ya fadi ma’anar ba zai sani ba. Hanyar rubutu ce ta fadakar da wanda bai yi karatun boko ba, ko bai san haruffan boko ba, ya iya sanin naira nawa ne. Akwai littafai da dama har da Baibul da kiristoci na duniya suka rubuta da larabci ko haruffan larabcin da wanda bai sani ba sai ya dauka Alkur’ani ne.

3. Ofishin Kasafi ya ce da wuya hukumomi guda 428 na gwamnatin tarayya, su iya biyan ma’aikatansu albashin wannan watan da muke ciki na Nuwamba saboda ba kudi.

4. Majalisar Wakilai ta umarci Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya, ya mika wa Shugaban Majalisar sunayen duk ‘yan sandan da aka kashe sakamakon zanga-zangar da aka yi domin biyan iyalansu diyya.

5. Wani dan rajin kare hakkin bil’Adama, Mista Okeke ya kai jiga-jigan zanga-zangar #ENDSARS su wajen 47, makadansu da marayansu, kotu, saboda zargin sun masa barna.

6. A yanzun cututtuka irin su yelofiba da maleriya da kwalara ke ta kisa. Na baya-bayan nan shi ne mutane takwas da yelofiba ta yi sanaddiyar mutuwarsu a jihar Bauci.

7. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos, mutum 180 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 74
Oyo 41
Abuja 19
Kaduna 19
Bauci 12
Ogun 7
Ribas 4
Kuros Ribas 2
Edo 2

Jimillar da suka harbu 64,516
Jimillar da suka warke 61,737
Jimillar da ke jinya 2,597
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,162

8. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na yi wani kuskure a rubutuna na jiya. Na ce an rada wa ginin rediyo da talabijin na KSMC da ke titin Wurno daura da titin Rabah da ke Badarawa Kaduna, sunan marigayi Yusuf Ladan. To sunan Muhammadu Ladan ne ba Yusuf Ladan ba.

Kuma har ila yau shi Yusuf Ladan idan ya ji kana karanta labaru ka ce SARKI YA KOKA sai ya sa a kira ka ofishinsa. Ya tambayeka ka taba ganin Sarki na kuka? Kodayake na san wani zai ce ai kuwa a litinin da ta gabata wajen nadin Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya ga yana jawabi yana zubar da hawaye. Ba irin wannan kukan Dan Iya yake nufi ba. Dan Iyan Zazzau
na nufin kukan wahala.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply