Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 13.06.2020

Taskar Guibi: 13.06.2020

165
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da daya ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Jiya take Ranar Dimukradiyya a Nijeriya inda shugaban kasa Muhamnadu Buhari ya yi wa al’umar kasar nan jawabi kai tsaye ta gidajen rediyo da talabijin da karfe bakwai na safe. A jawabin ya jinjina wa gwarazan dimukraddiya, da tabo nasarori da kuma kalubalen da aka yi fama da su bayan hawansa mulki, bangaren aikin gona, da na tsaro, da tattalin arziki, da siyasa da sauransu. Har ya ce duk da matsalar da ake ciki ta kwaronabairos kudaden da Nijeriya ke da su na ketare a watanni uku na farkon shekarar nan, kudaden sun karu daga dala biliyan talatin da uku da kusan rabi 33.42 zuwa dala biliyan talatin da shida.

2. Kasar Indiya ta kwashe ‘yan kasarta da ke Nijeriya su dari uku da goma sha biyu.

3. Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a yi asarar ayyuka guda miliyan goma sha uku a Nijeriya sanadiyyar kwaronabairos.

4. Kotu ta ba da umarnin a tsare wani dan jarida da ya soki ministan labaru Lai Mohammed.

5. Hukukar EFCC ta ce ta mayar wa jihar Imo wata naira biliyan uku ba wasu mutsa-mutsai da ta karbo daga hannun tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha. Sannan ofishin hukumar da ke nan Kaduna ya ce an kai wa ofishin korafe-korafe na ba daidai ba da kudi har guda dubu hudu, da dari takwas da saba’in da daya daga Yunin bara zuwa Yunin bana.

6. Tsohon gwamnan jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa ya kawo shawarar a hukunta dukkan wadanda ke da hannu a rushe zaben ranar goma sha biyu ga watan Yuni da ake kyautata zaton Abiola ne zai lashe shi.

7. Jam’iyyar APC ta jihar Edo ta ce gwamna Obaseki bai cancanci ya tsaya takarar fid-da-gwani na wanda zai tsaya wa jam’iyyar APC takarar gwamna ba, saboda takardunsa na shaidar karatu har da na bautar kasa suna da matsala. Sai dai ya ce soki-burutsu ne, wata majiyar ma na cewa ya tatkata inasa-inasa da mukarrabansa sun fice daga APC sun koma PDP.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na nan suna ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

9. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 627 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 229
Abuja 65
Abiya 54
Barno 42
Oyo 35
Ribas 28
Edo 28
Gwambe 27
Ogun 21
Filato 18
Delta 18
Bauci 10
Kaduna 10
Kwara 6
Nasarawa 4
Inugu 4
Sakkwato 3
Neja 3
Kabbi 3
Yobe 1
Kano 1

Da ke nufin kowacce jiha ta kasar nan tana da alkaluma kamar haka:

Legas 6,840
Abuja 1,162
Kano 1,049
Ogun 544
Edo 518
Ribas 482
Oyo 469
Barno 423
Katsina 411
Bauci 402
Kaduna 402
Gwambe 320
Jigawa 314
Delta 243
Ebonyi 152
Abiya 151
Kwara 149
Filato 148
Nasarawa 132
Sakkwato 132
Imo 114
Zamfara 76
Ondo 62
Anambara 53
Yobe 53
Kabbi 50
Oshun 50
Neja 49
Akwa Ibom 45
Adamawa 42
Inugu 39
Ekiti 30
Binuwai 22
Taraba 18
Kogi 3
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 15,181
Jimillar wadanda suka warke 4,891
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 399
Jimillar wadanda suke jinya 9,891

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Ku dake shi
Ku taka wuyansa
Ku bugi hancinsa
Daki hancinsa.
Ci uban shi
Dan bura uba
Ya ci ubanshi
Wanne dan bura uba ne
Munafiki ne
Uwarka
Yau mun gano ka.
Ku tadiye shi

Lokacin da ‘yan Majalisar Dokoki ta jihar Kaduna ke bai wa hammata iska ke nan ko yi wa waninsu taron-dangi kafin tsige mataimakin shugaban majalisar da maye gurbinsa da wani.
Mai son ganin bidiyon ga shi nan a kasan wannan rubutu na dandalina na fesbuk, don ban sani ko bidiyon zai iya raka rubutun zuwa sauran dandali daban-daban da za a tura rubutun nawa na yau ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply