Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 13.11.2020

Taskar Guibi: 13.11.2020

613
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin da bakwai ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1. Na lura zakarun yanzun ko dimuwa ce? Karfe biyun dare suke fara cara maimakon su bari karfe hudu ya yi lokacin da ladan ke kiran assalatu. Su ma ladanan na lura wasunsu tun karfe uku da rabi da ‘yan mintoci na dare suke soma kiran assalatu, maimakon su bari karfe hudun asubah ya yi. Ko asubah na farawa karfe biyu ko uku ne?

2. A nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fito an jima da safe, domin duba shafukana, da ke dauke da labarun da na kawo muku daga Juma’ar da ta gabata zuwa jiya Alhamis.

3. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na yanzun, Jaja, ya musu allawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

4. Gwamnatin Tarayya ta ce sam ba za ta yi amfani da wani sabon tsarin biyan albashi a jami’o’i ba. Da ke nuna zaune ba ta kare ba, tsakanin malaman jami’a da Gwamnatin Tarayya. Su kuwa ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

5. Akwai sabbin harbuwa da kwanorabairos mutum 212 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 71
Imo 26
Filato 26
Abuja 19
Ondo 17
Kaduna 14
Ribas 9
Oyo 9
Katsina 6
Oshun 4
Bauci 2
Ekiti 2
Nasarawa 2
Ogun 2
Kano 1
Kwara 1
Taraba 1

Jimillar da suka harbu 64,728
Jimillar da suka warke 60,790
Jimillar da ke jinya 7,776
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,162

6. ‘Yan kungiyar Boko Haram da sauran mahara na ci gaba da cin karensu babu babbaka, a jihar Yobe da Zamfara, da Katsina, da Kaduna da Neja har da Sakkwato, da Nasarawa. A baya-bayan nan sun kai mamaya wani kauyen jihar Yobe, sannan a mutanen Bukuyum, da na Anka, da Maru, daga wadanda ‘yan bindiga suka sa wa haraji kafin su je gona girbi, ko sun biya sai sun yi kidinafin din su, sai wadanda aka yi kidinafin sarkin garinsu da iyalansa, sai fiye da dubu goma da suka tsere daga garinsu saboda mahara, da dai sauran bala’o’i daban-daban da suke zargin gwamati ta gaza wasunsu ke ma zargin babu gwamnati a Nijeriya.

7, Sojoji sun ce sun kashe wasu ‘yan ta’adda su biyar tare da kwato tarin makamai a Arewa Maso Gabashin Kasar nan. Har ila yau hukumomin soja sun yi shelar suna neman su Shekau da Albarnawi da wasu ‘yan Boko Haram su wajen tamanin da hudu ruwa a jallo.

8. ‘Yan Nijeriya da ke Ghana karkashin inuwar kungiyar ‘yan Nijeriya da ke kasuwanci a Ghana, sun aiko wa da Gwamnatin Nijeriya takardar neman ceton ransu daga cin zarafinsu da ake ci gaba da yi a Ghana. Tare da rokon a kwaso su zuwa gida.

9. Tsohon shugaban mulkin soja da gwamnatin farar hula na Ghana Jerry Rawlings ya riga mu gidan gaskiya sakamakon harbuwa da kwarona. Har Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da gaisuwarsa ta ta’aziyya. Ya yi mulki daga 1981 zuwa 2001 kuma an ce shi ya yi maganin manyan gafiyoyin da suka addabi Ghana a lokacinsa.

10. Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, ya ce ‘yan kwangila su fiye da dubu uku bangaren samar da gidaje, ke bin ma’aikatarsa Naira Biliyan 69.9. Kuma kasafinsa na shekarar 2021 Naira Biliyan 76.45 ne. Saboda haka bai san yadda zai yi ba.

11. An rantsar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa Philip a Benin don zarcewa da mulkin jihar Edo. Sai dai na lura a ranar rantsar da shi jiko ko wa’adi na farko matarsa ta fi shi tsawo. A rantsarwar jiya ya fi matar tsawo.

12. Wani soja jiya ya mayar da martani a dandalina a kan labarin majalisar wakilai da ta nemi shugaban ‘yan sanda ya mika sunayen ‘yan sandan da aka kashe a lokacin zanga-zangar da aka yi, don biyan iyalansu diyya. Shi sojan ya ce su kuma sojojin da aka kashe lokacin zanga-zangar fa?

Mu wayi gari lafiya. Mu yi juma’a lafiya.

Af! Can na ga wata sanarwa daga hukumar tara haraji/kudaden shiga ta jihar Kaduna da ke cewa za a bullo da harajin naira dubu daya na raya kasa, da kowanne mazaunin jihar Kaduna da ya kai munzalin biya, zai dinga biya sau daya tal a duk shekara.
Hmm! To ni a duk wata ina biyan naira dubu ashirin da daya, da naira dari da takwas, da kwabo saba’in da shida harajin da ake cire mun a albashi na gwamnatin jihar Kaduna. A duk shekara ina biyan naira dubu dari biyu da hamsin da bakwai, da naira dari biyu da sittin da tara, da kwabo goma sha biyu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply