Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 13.12.2020

Taskar Guibi: 13.12.2020

638
0

Assalamu alakum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin da bakwai ga watan Rabiul-Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Disamba, shekarar 2020.

1. Labarin da ya fi daukar hankali jiya musamman a soshiyal midiya, shi ne na wasu ‘yan bindiga da suka je makarantar sakandare ta gwamnati ta Kankara da ke jihar Katsina, suka kwashi yara ‘yan makarantar, shigen na ‘yan matan Chibok. Dalibai ne kusan su dari takwas, dari hudu da talatin da shida sun dawo, ana neman wasu da ba a san yawansu ba, da ake kyautata zatton sun tafi da su ne. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da wannan lamari, ya kuma umarci sojoji da ‘yan sanda su bi ‘yan bindigan daji. Masari hakuri yake ta ba iyaye, ya kuma ba da umarnin rufe duka makarantun kwana da ke jihar. Ita kuwa PDP cewa ta yi tunda Shugaban Kasa Buhari ya kasa sauke ainihin aikinsa na kare lafiya da rayukan al’umar kasa, to ya sauka daga mulkin ya ba da waje. Mutanen yankin sun shaida wa BBC Hausa, cewa su dama sun saba kusan duk kwana biyu sai kidinafas, da makasa sun bakunce su.

2. An sako dan majalisar dokoki na jihar Taraba da aka yi kidinafin a muhallinsa da ke Jalingo.

3. Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum hudu a Angbade ta jihar Binuwai, suka ji wa da dama rauni. Na kuwa ga Ortom wato Gwamnan jihar, ya isa Angbaden yana hucin ba fa zai lamunta ba.

4. Yau za a yi wa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai gwajin kwaronabairos, saboda yana tunanin ya harbu, saboda hulda da kuma musabahar da ya yi da jama’a, da daga bisani aka gano sun harbu. Tuni gwamnan ya killace kansa da kansa. Shi ma Gwamnan jihar Legas, Olu ya harbu kuma yana killace.

5. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 617 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 225
Abuja 181
Kaduna 125
Adamawa 24
Nasarawa 20
Kano 12
Ribas 8
Edo 4
Bayelsa 3
Ogun 3
Filato 3
Akwa Ibam 2
Delta 1
Sakkwato 1
Jimillar da suka harbu 72,757
Jimillar da suka warke 64,850
Jimillar da ke jinya 5,713
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,194

6. Yau 43 ga watan NUWAMBA ga yawancin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, saboda har yau ba su ga dilin-dilin na watan Nuwamba ba, ga watan Disamba ya lula.

7. Malaman jami’a sun ce GwamnatinTarayya suke jira ta motsa, sai su ma su motsa, yara su koma makaranta.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekarar da ke shirin kankama, sun cika shekara hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba sa korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ‘yan siyasa na musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura, ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

10. Shekaranjiya da daddare Sam Nda Isaiah mamallakin jaridar nan ta Leadership ya riga mu gidan gaskiya. An haife shi a 1962, ya ma taba tsayawa takarar neman shugabancin kasar nan. Shugaban Kasa Buhari, da mataimakinsa Osinbanjo, da Ahmad Lawan da Femi duk shugabannin majalisun dokoki na kasa, da sauran fitattu da mashahuran ‘yan Nijeriya, sun nuna kaduwarsu da rashinsa da aka yi.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Wasu ke tambayata, me ya sa kwaronabairos ta kasa shiga jihar Kogi ne? Ni kuma na ce watakila tana tsoron Yahya Bello ne. Wasu kuma ke tambayar me ya sa yawan masu harbuwa a jihar Kano ba ya kai na jihar Kaduna ko kusa ne, alhali an ma fi samun gwamutsuwar jama’a a Kano kuma sun ma fi Kaduna yawan jama’a? Na ce watakila! Watakila!! Watakila!!! Watakila!!!! Watakila!!!!!

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply