Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 14.01.2021

Taskar Guibi: 14.01.2021

152
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, talatin ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha hudu ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Donald Trump shi ne shugaban Amurka na farko da aka taba tsigewa har sau biyu. Saboda bore da tutsu irin na jaki, da yake ta yi na shi ba zai sauka daga kan mulki ya ba Biden sabon shugaban Amurka ba.

2. Fadar Shugaban Kasa ta tsawata wa wadanda suka butsare suka umarci Mathew Hassan Kukah, ko ya nemi gafara a kan kalaman da ake zargin ya yi, ko ya tarkata inasa-inasa ya bar Sakkwato birnin Shehu. Fadar ta ce kowa yana da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa a matsayinsa na dan kasa, ba tare da wani bore ba, kuma ba tare da an tsangwame shi ba.

3. Hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO, ta fitar da sakamakon jarabawarta, da dalibai suka rubuta a shekarar 2020. Sai dai wadanda suka yi wa dokokinta bore, ta soke ko rike sakamakon jarabawarsu.

4. Yau ma’aikatan jami’o’i manyansu da kananansu, ban da malaman jami’o’in, za su cika yini na uku suna bore, a kan IPPIS, da ariyas na sabon albashi da suka kusan shekara biyu suna bi, da yadda suke zargin aka yi rabon ganima aka barsu da kuturun bawa tsakaninsu da malaman jami’o’i da sauran korafe-korafensu.

5. Jiya tsofaffin sojoji manyansu da kanana, suka yi bore a Abuja, a kan ariyas na fansho na watanni da suke bi, da na karin albashi mafi karanci, da wasu alawus na iya harba bindiga, da ya kamata a ce ana biyansu, don kada su yi amfani da kwarewarsu ta iya harbi, su yi bore su yaki gwamnati.

6. Ma’aikatan hukumar da ke yi wa ‘yan kasa rajista, na korafin su fa an sa su sun janye boren aiki, amma har yau ba su ga Pantami ba. Sun ce idan suka ji shiru, za su watsar da aikin su ci gaba da bore.

7. Malaman jami’a na ci gaba da korafin su fa har yanzun ba su gani a kasa sosai kamar yadda gwamnati ta musu alkawari suka hakura da borensu ba.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i, na Gwamnatin Tarayya, na tunanin ko sai sun yi bore ne, kafin gwamnati ta biya su ariyas na sabon albashi da suka kusan shekara biyu suna jira?

9. Wasu na cewa da alama boren kungiyar Boko Haram, na hana karatun Boko bai yi nasara a jihar Bauci, kamar yadda ya yi nasara a wasu jihohin Arewa ba. Domin Dafta Aliyu U. Tilde kwamishinan ilimi na jihar, ya ce za su bude makarantunsu ba fashi.

10. A jihar Kaduna, kwaronabairos ce ta yi nasara a nata boren, inda ta sa gwamnatin jihar, ta ce ba ranar komawa makaranta a yanzun tukuna.

11. Kwaronabairos ta yi wa likitoci har ashirin bore a jihar Kwara, ta harbe su.

12. Cutar ta kwarona, na ci gaba da bore a kasa bakidaya, har mutum 1,397 sun harbu a jiya kawai da alkaluma a jihohi kamar haka:
Legas 542
Abuja 131
Oyo 120
Ribas 113
Filato 111
Kaduna 71
Kwara 71
Akwa Ibom 34
Sakkwato 31
Binuwai 28
Ogun 27
Kano 26
Kabbi 17
Oshun 12
Anambara 11
Delta 10
Gwambe 10
Bayelsa 9
Barno 9
Edo 8
Ekiti 3
Jigawa 2
Katsina 2
Jimillar da suka harbu 103,999
Jimillar da suka warke 82,555
Jimillar da ke jinya 20,062
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya, 1,382

13. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, da ke ta hakuri da ‘yan siyasa, tare da kaurace yi musu bore, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin gyaran gada. A lokacin yakin neman zabe ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Ta labarin Dare Dubu Da Daya, bari in tsaya a nan, daga barin zance mai dadi, kafin lokaci ya yi mun bore.

Af! Yau fa labarun kowanne da BORE a cikinsa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply