Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 14.02.2021

Taskar Guibi: 14.02.2021

71
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, biyu ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 14 ga watan Fabrairu, shekara 2021.

1. Gwamnatin jihar Oyo ta rufe Kasuwar Sasa Ibadan, da kafa dokar hana walwala, sakamakon wata takaddama da ta auku tsakanin wani bahaushe dan dako, da wata bayarabiya da ya daukarwa dakon kaya, a karshe sai rikici tsakaninsu, rikici ya rikide na kabilanci, aka yi zargin an kashe Hausawa da dama, da lalata dukiyoyinsu, kama daga gidaje, zuwa motoci da rumfunansu.

2. Masu kaso da raba wa jihohi alkaluman kwarona, jiya sun ba jihohin Nijeriya 1,143 kamar haka:

Legas 319
Abuja 157
Kwara 90
Oyo 74
Inugu 72
Nasarawa 69
Imo 58
Oshun 51
Gwambe 49
Kaduna 31
Edo 23
Katsina 23
Kabbi 23.
Ogun 22
Kano 19
Ribas 19
Ebonyi 18
Filato 14
Delta 7
Ekiti 5

Zuwa yanzun ta ba Nijeriya 145,664
Ta ce wadanda suka warke, 120,399
Ta kasa wa masu jinya 23,518
Ta ce mutum 1,747 ne ya mutu.

3. Gwamnatin Tarayya ta raba wa mata su dubu hudu, naira miliyan 80 a jihar Neja.

4. Wasu Fulani masu yawan gaske da ake ta kwarzaba a jihar Neja, sun yi kaura jihohi daban-daban ana ta korarsu, a karshe suka nufo jihar Kaduna, aka ba su masauki.

5. Kidinafas da suka yi kidinafin wata yarinya a Abuja, sun bukaci mahaifin yarinyar ya biya su ne da kwandalar bitukoyin ba da naira ba. Kwatankwacin dala dubu goma sha biyar. Haka ya biya suka sakota.

6. A jihar Taraba kidinafas sun sako wani mai taimaka wa gwamnan jihar da suka yi kidinafin kwanakin baya.

7. Makasa sun kashe wani uba da dansa a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, wasu makasan suka tare wata mota da mutum uku a ciki, suka kashe su a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna

8. Sojoji na sama, sun ce sun dakile wani hari da wasu ‘yan fashin daji suka so kaiwa yankin Birnin Gwari, inda suka musu kwanton bauna, suka kashe su da dama. Sai dai sun ce an ji wa wasu sojojin nasu rauni.

9. Babban mai ba da shawarar bangaren tsaro na kasa ya gana da sabbin hafsoshin tsaron kasar nan.

10. An damke 40 daga cikin masu zanga-zangar #occupylekki a Legas.

11. Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, na ta samun nasara a ‘yan kwanakin nan, ko don ta samu sabon shugaba ne?

12. Nepa! Nepa!! Nepa!!! Talakan Nijeriya na ci gaba da biyan kudin zama a duhu, da a yanzun zaman ke da tsadar gaske.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka dade da biyan sauran ma’aikata, amma su har yau shiru.

14. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah ka mana maganin makiya da ke cikin dangi Amin. Ga su danginka ne, tsatso guda, zuri’a daya, amma ba sa kaunarka ko kadan. Da ire-irensu ake hada baki a shirya maka wani mugun abin, har da kidinafin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply