Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 14.10.2020

Taskar Guibi: 14.10.2020

368
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, ashirin da shida ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha hudu ga watan Oktoba na shekarar 2020.

1. A karshe dai Gwamnatin Tarayya ta amince yau za ta gwada ingancin tsarin biyan albashi da kungiyar malaman jami’a ASUU ta kera abinta, bayan ta ki amincewa da IPPIS da wasu suka kera ake kokarin kakaba mata. Da ke nuna malaman jami’a sun yi nasara a kan gwagwarmayarsu ta kin amincewa da IPPIS.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya sanar da sunan sabuwar rundunar SWAT da ta maye gurbin SARS da aka rusa, tare da umartar dukkan jami’an haramtacciyar SARS su kai kansu shalkwatar ‘yan sanda da ke Abuja don duba lafiyar kwakwalwarsu da ta jiki, kafin a yi batun yi musu sabon horon yadda ake so su kasance.

3. Lauyoyi a Legas sun bi sahun masu zanga-zangar sai an kawo canji a aikin dan sanda. Har kungiyar ta lauyoyi ta yi tir da kisan da ake zargin ‘yan sanda sun yi wa masu zanga-zangar kawo karshen SARS.

4. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce ai Gwamnatin Tarayya ta biya bukatu guda biyar da masu zanga-zangar ENDSARS suka gabatar, saboda haka bai ga dalilin ci gaba da zanga-zangar ba.

5. Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya ce bai kamata a zubar da jinin masu zanga-zangar neman kawo sauyi a aikin ‘yan sanda ba.

6. Gwamnan jihar Barno Zulum ya ce shi ya ga alfanun SARS saboda haka a tura masa karinsu jiharsa.

7. Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Aminesti ta ce ‘yan sanda sun kashe mutum goma cikin masu zanga-zangar ENDSARS, sai dai ‘yan sanda sun ce su ne ma masu zanga-zangar suka kashewa ‘yan sanda biyu da ji wa uku rauni.

8. Shugaban Kasa Buhari ya nada Lauretta da ke taimaka masa bangaren kafofin watsa labaru, a matsayin kwamishinar hukumar zabet ta kasa, inda PDP ta ce ba ta yarda ba, domin za ta taimaka wa APC murdiyar zabe.

9. Majalisar Dattawa ta amince da nadin wasu alkalai takwas na kotun daukaka kara zuwa kotun koli.

10. An ci gaba da shari’ar Hamisu Wadume da wasu mutum shida.

11. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 225 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 165
Abuja 17
Ribas 13
Ogun 12
Neja 8
Delta 4
Ondo 2
Anambara 1
Edo 1
Ekiti 1
Kaduna 1

Jimillar da suka harbu 60,655
Jimillar da suka warke 52,006
Jimillar da ke jinya 7,533
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,116

12. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata bakwai ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Jiya wuraren karfe biyar na yamma daidai titin Katsina, daura da titin Maiduguri idan ka fito titin Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna, na ga motoci biyu na sabuwar rundunar tsaro ta jihar Kaduna, suna jiniya da tukin ganganci da layi, da kwanto da mota suna barazana ga sauran masu ababen hawa ire-irena da ba kowa ba. Saura kiris kuwa da sun buge wani mai babur, da goga wa wata mota. Har wadanda ke cikin motata ke cewa da su Gwamna El-Rufai ya taimaka ya kai su tsaron Kidandan da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da ‘yan bindiga ke ta addabarsu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nieriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply