Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 14.11.2020

Taskar Guibi: 14.11.2020

362
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, ashirin da takwas ga watan Rabi’ul Awwal shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha hudu ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

1. Kugiyar Dillalan Manfetur da ke Zaman Kansu ta Kasa IPMAN a takaice, ta umarci ‘ya’yan kungiyar su kara kudin man kowacce lita zuwa naira dari da saba’in 170 daga jiya. Saboda su ma an kara musu kudin man da ake sayar musu. A takaice dai an kara kudin man fetur, kuma da ma jiya na ji Ministar Kudi Shamsuna, na korafin kayayyaki sun yi tsada ne a kasuwa saboda masu motocin sufuri, na sayen fetur da tsada suna zuba wa motocin nasu.

2. Karin kudin wutar lantarki dai ya zauna. Kafin karin idan ka sayo katin wuta na naira dubu daya, za a ba ka awo 36 na wutar wato 36 units kuma zai maka kwana biyu. To a yanzun idan ka ba da naira dubu daya da dari biyar, za a ba ka awo 26 wato 26 units kuma dandanan za ka ga ya kare. A wata sai ka sayi katin naira dubu goma sha biyar da dari biyar. Wadanda ba su da mitar iya-kudinka-iya-shagalinka kuwa, suna biyan naira dubu ashirin da tara zuwa talatin. Ka ga ana cutarsu naira dubu goma sha hudu zuwa sha biyar a duk wata.

3. Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna, ta yi korafi a kan harajin Naira Dubu Daya na raya kasa da Gwamatin jihar Kaduna ta bullo da shi, cewa duk wani baligi da ke zaune jihar zai biya. PDP ta ce babu tausayi a lamarin gwamnatin jihar Kaduna. Ta ce an rushe wuraren sana’o’in jama’a, an kori ma’aikata aiki har yau ba a biya su hakkokinsu ba, ga haraji na kowanne gida, ga kudin fansa da talaka ke biyan kidinafas, a jihar Kaduna. Ga wannan haraji ga wancan haraji, yau kuma a ce gwamnatin ta dora wa kowa harajin Naira Dubu Daya, PDP ta ce rashin imani ne.

4. Gwamnan jihar Kwara, shi ma ya yunkura zai soke kudin fansho da ake biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu na jihar.

5. Wani bangare na kungiyar dalibai da ke karatu a manyan makarantu, ya ba Gwamnatin Tarayya wa’adin mako guda ta sasanta da malaman jami’a su koma aiki ko su nuna wa gwamnatin fushinsu.

6. Jiga-jigan zanga-zangar #ENDSARS sun nemi kotu ta tilasta wa Babban Bankin Nijeriya bude musu ajiyarsu ta banki da ya dode musu. (To defreez their freezed accounts).

7. Wani kwale-kwale ya kife da wasu mutum ashirin da uku a kauyen Zango Majiya da ke jihar Bauci, sha takwas suka riga mu gidan gaskiya, aka ceto biyar.

8. Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata CCB a takaice, ta nemi Ibrahin Magu ya hallara a gabanta, da takardarsa ta farko ta daukar aikin gwamnati, da duka takardunsa na biyan albashi wato PAYSLIPS, da takardun shaidar dukkan kaddarorin da ya mallaka, da wadanda ya gina da wadanda yake kan ginawa ko bai gina ba tukuna.

9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

10. Da alamu al’umar kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna ta auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta mata alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da al’umar ke samu ta haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya mata alkawarin idan ta zabe shi zai gyara mata. Ta zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara mata ba.

11. Akwai sabbin harbuwa da kwarona mutum 156 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 70
Abuja 22
Kaduna 18
Ribas 11
Filato 11
Ogun 10
Bauci 3
Katsina 3
Kano 2
Ekiti 1
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 64,884
Jimillar da suka warke 63,936
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,163
Jimillar da ke jinya 215.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau ma zan sake waiwayar wakar nan ta Dafta Mamman Shata da yake cewa :

MU/KU GARGADI MAI GINA RAMIN MUGUNTA. IN ZA KA GINA RAMIN MUGUNTA, TO GINA SHI DAIDAI KAI DON WATAKILA KAI KA AUKA, Mu GARGADI MAI GINA RAMIN MUGUNTA.

Sai kuma wani Ingishi da ke cuwa :

If you are living in a glass house, do not throw stones.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply