Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 15.01.2021

Taskar Guibi: 15.01.2021

143
0

Assalamu Alakaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, daya ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Janairu, na 2021.

1. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a, da za ta fito an jima da safe, domin duba shafukana, da ke dauke da labarun da na kawo muku daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis. Haka nan akwai jaridar Muryar ‘Yanci, ta rediyo da talabijin na Libati.

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda ya kira ELITES, da wasunmu ke fassara su da ‘yan boko, wasu kuma ke fassara su da idon gari, da in za su soki gwamnatinsa, su dinga yi wa gwamnatin tasa adalci. Ya ce su duba inda kasar take a da, da inda take a yanzun su gani daya ne?

3. Gwamnatin Tarayya ta ce ranar 18 ga watan nan da aka tsayar don bude makarantu ba fashi za a bude. Sai dai wasu jihohi ne, da suka ce babu ranar bude nasu makarantun.

4. Gwamnatin Tarayya ta yi karin hasken babu batun kulle karo na biyu.

5. Sojoji sun ce sun kashe ‘yan Boko Haram, su 64 a jihohin Barno da Yobe.

6. Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, ta bukaci Gwamnatin Tarayya, ta bai wa Mathew Hassan Kukah kariya, wato tsaronsa kada wani abu ya same shi, daga masu masa barazanar ya bar Sakkwato.

7. Ana zargin Amotekun na cin zarafin fulani da sauran al’umar Arewa da ke jihohin Yarbawa har da kisan wasu fulani bakwai a baya-bayan nan. Sai dai Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya musanta.

8. Kungiyar ma’aikatan jami’o”i manyansu, da kananansu NASU da SSANU, sun kammala boren da suka yi na yini uku jiya. A kan IPPIS, da batun kason da aka yaga musu na kudi, da ariyas da suke bi na sabon albashi.

9. A jihar Zamfara, wadanda suka yi kidinafin wasu yara shida, sun nemi sai an ba su naira miliyan hamsin kafin su sako su.

10. A jihar Kaduna, wasu kidinafas ne suka kashe mutum biyu a kauyen Chikaji da ke yankin karamar hukumar Igabi, kwanaki kadan da kashe wasu mutum uku a dai wannan karamar hukuma.

11. Wani rahoto da BBC Hausa ta bayar jiya da rana, na cewa jami’an tsaro sun je gidan Shek Dahiru Bauci da ke baifas Kaduna, da daddare, suka kwashi wasu almajirai da ke harabar.

12. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan, ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan, na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dau alkawari a lokacin yakin neman zabe.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i, duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da suke korafin an ba sauran ma’aikata, su an hana su.

Mu wayi gari lafiya, mu yi Juma’a lafiya.

Af! Yau fa Juma’a, a ci gaba da dagewa da addu’a Allah Ya mana maganin abin da ya dame mu Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply