Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 15.02.2021

Taskar Guibi: 15.02.2021

94
0

Assalami Alaikum barkanmu da asubahin Litinin, uku ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Fabrairu, na 2021.

1. Jama’a na ci gaba da korafin gidan talabijin na TVC, da Channels, da AIT, da ARISE da sauransu, da yake nasu ne, ba su mayar da hankali ga ba da rahoton abin da yarbawa suka yi wa Hausawa a Kasuwar Sasa ba. Ana ta korafin da a ce Hausawa ko Fulani ne suka yi wa Yarbawa haka a nan Arewa ko a can yankin, da yanzun sun dau dumi suna ta sa rahoton da sharhi iri-iri kai ka ce tashin duniya ne. Masu korafin suka ce da yanzun kungiyoyinsu da lauyoyinsu, da ‘yan bokonsu, sun tasa Hausawa da Fulani a gaba ba sararawa.

2. Mataimakin Shugaban Kasa Osinbanjo ya yi kiran a zauna lafiya a tsakanin ‘yan kasuwa Hausawa da Yarbawa da ke Ibadan. Haka nan gwamnan jihar Oyo da na jihar Ondo sun ziyarci kasuwar da aka yi wa Hausawa barna, da kisa, da kona musu motoci da muhalli, da rumfuna. Rahotanni na nuna duk da an sa dokar hana walwala, Yarbawa sun ci gaba da kai wa Hausawa hari da lalata musu dukiya. A yanzun haka dubban Hausawa sun fake suna gudun hijira a gidan Sarkin Hausawa.

3. Wasu na ci gaba da kiran tunda auren tsakanin Kudu da Arewa ya gagara, a raba mana kowa ya san inda dare ya masa.

4. Wasu na ta rubuce-rubuce cewa Bahaushe ya shiga uku. Nan Arewa Fulani kidinafas, da ‘yan fashin daji, da Barebari ‘yan Boko Haram, na ta farautarsa a gida da daji su kashe na kashewa, su yi wa iyalansa fyade, da kona masa gari da dukiya, da yi masa yankan rago, da biyan kudin fansa. Can kuma a kudu ana ta farautarsa ana kashewa.

5. Wani rahoto na nuna kidinafas sun tare wata motar daukar fasinja ta hukumar sufuri ta jihar Neja, a karamar hukumar Rafi, ta fito daga Kwantagora za ta Minna, suka yi kidinafin fasinjoji 18 da ke ciki, suka kyale wata mai goyo da goyon nata, ba su tafi da ita ba.

6. Sojoji sun ce sun kashe wasu manyan kwamandojin Shekau su biyu, da suke nema ruwa a jallo, Abdul-Bas da Ibn Habib.

7. Mai ba da shawara bangaren tsaro na kasa, da sabbin hafsoshin tsaro, da gwamnonin Arewa maso yammacin kasar nan, za su yi taro a Kaduna, don gano bakin zaren magance matsalar tsaro da ke addabar yankin.

8. A shekarar 2020 kwamitin nan mai kaso da raba kudade duk wata ga gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi FAAC, ya ce ya hankada musu naira tiriliyan biyar ba wasu ‘yan canji, 4.75trn.

9. Hukumar da ke kaso da raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos a kullum, ta so ta yi wa jihohi kwauron cutar jiya, don 520 kawai ta raba musu kamar haka:

Ondo 120
Barno 41
Ebonyi 37
Binuwai 33
Filato 30
Abuja 29
Nasarawa 25
Ogun 25
Edo 24
Oshun 24
Katsina 22
Neja 20
Kwara 14
Ekiti 13
Yobe 10
Bayelsa 1
Jigawa 1

Jimillar da hukumar ta raba zuwa yanzun 146,184.
Jimillar da ta kasafta na wadanda suka warke 120,838.
Jimillar da aka ware wa masu jinya 23,594.
Alkaluman da ta kebe wa matattu 1,752.

10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na Kudan, Jaja, da wa’adinsa ke shirin karewa, ya daure ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Sun cika alkawari sun zabe shi, wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.

11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka dade da biyan sauran ma’aikata, su kuwa har yau shiru.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wani rubutu da na yi ranar 14 ga watan Fabrairu na shekarar 2016, wato biyar ke nan.

“Ni dai daga daya ga watan nan na Fabrairu da aka kara kudin wuta babu wata inganta da wutar ta yi sai ma kara tabarbarewa da ta yi. Wannan zalunci har ina? Akwai ministoci biyu da nake so Baba Buhari ya sauke su don ba su da amfani kuma suna yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa. Ministan lantarki da karamin ministan mai. Gaskiya su tarkata inasu-inasu su san inda dare ya musu tun rana ba ta fadi ba”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply