Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 15.06.2020

Taskar Guibi: 15.06.2020

140
0
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da uku ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.
1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi gaisuwar ta’aziyyar Ibidunmi Ighodolo matar fasto Huah Ighodolo da ta riga mu gidan gaskiya a wani otel.
2. An bayyana cewa babu abin da ya auku ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sakamakon wata hatsaniyar da ta auku a cikin fadar shugaban kasa ranar alhamis tsakanin iyalansa da har ta kai ga an harba bindiga da tsare wasu mukarraban.
3. Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wuraren Guibio har ya shafi bangaren ayyukan jinkai.
4. Sojojin sama sun dakile wani sabon hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai Barno. Sannan sojoji sun farmaki ayarin kwamitin yaki da kwaronabairos na jihar Barno, har mutum daya ya riga mu gidan gaskiya.
5. Wani fadan kabilanci a jihar Binuwai ya yi sanadiyyar kashe mutum a kalla goma, ashirin ba a san inda suke ba.
6. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari Mongunu da ke jihar Barno, suka kashe sojoji da farar hula.
7. Wasu ‘yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare ‘Yan Kara da ke jihar Katsina, suka kashe mutane da dama, suka yi kidinafin wasu, a yankunan Daudawa da su Funtuwa, da Faskari da Kankara ga jama’a na ta gudun hijira daga garuruwansu.
8. Shalkwatar Tsaro ta ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe fiye da mutum tamanin da daya a Guibio da ke jihar Barno.
9. Wata gada da ta rifta sakamakon ruwan sama a jihar Kwara, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da bacewar wasu mutum biyu.
10. Shugaban Kasar Ghana Akufo-Addo ya sanar da za a bude jami’o’i da sauran manyan makarantu da ke kasar a yau litinin bayan kulle su sakamakon kwaronabairos.
11. Ana ci gaba da zanga-zanga a kasashen duniya irin su Jafan, da Jamus, da Niw Zilan da sauransu na taya Amurkawa da ke zanga-zangar Allah Ya tsine wa ‘yan sanda turawa da suka kashe George Floyd bakar fata.
12. Jiya kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 403 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Gwambe 73
Legas 63
Kano 46
Edo 36
Abuja 35
Nasarawa 31
Kaduna 17
Oyo 16
Abiya 15
Delta 13
Barno 13
Filato 8
Neja 7
Ribas 7
Inugu 6
Ogun 6
Kabbi 3
Ondo 1
Anambara 1
Imo 1
Da ke nuna kowacce jiha tana da jimillar alkaluma kamar haka:
Legas 7,103
Abuja 1247
Kano 1137
Edo 580
Ogun 559
Oyo 507
Ribas 489
Kaduna 446
Barno 438
Katsina 414
Bauci 410
Gwambe 410
Jigawa 317
Delta 267
Nasarawa 172
Abiya 166
Ebonyi 162
Filato 156
Kwara 150
Imo 136
Sakkwato 132
Zamfara 76
Anambara 65
Ondo 64
Inugu 57
Kabbi 57
Neja 56
Yobe 56
Oshun 50
Akwa Ibom 48
Adamawa 42
Binuwai 34
Bayelsa 32
Ekiti 30
Taraba 18
Kogi 3
Kuros Ribas 0
Jimillar wadanda suka harbu zuwa jiya 16,085
Jimillar wadanda suka warke zuwa jiya 5,220
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 420
Jimillar da suka yi saura suke jinya 10,445
Mu wayi gari lafiya.
Af sun dauka na manta da batun ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya ne, da ke ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi! Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply