Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 15.12.2020

Taskar Guibi: 15.12.2020

584
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da tara ga watan Rabiul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Disamba, na shekarar 2020.

1. Gwamna Masari na jihar Katsina, ya ce wadanda suka yi kidinafin yara ‘yan makarantar sakandare ta Kankara, sun kira waya an soma ciniki. Har wata ruwayar na nuna kidinafas din sun tsawata cewa ba fa sa so jirage sojan sama na damunsu da shawagi a inda suke. Wani yaro da ya samu ya kubuto daga hannunsu ya shaida wa BBC Hausa cewa su ‘yan makarantar da ke hannun kidinafas din sun haura dari biyar.

2. A jihar Neja, a yankin Ogu da Tegina, kidinafas sun yi kidinafin mutum goma sha tara, suka kashe mutum daya.

3. Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku, ya yi korafin tsaro na ci gaba da tabarbarewa.

4. Wasu sun tarwatsa taron da gamaiyar kungiyoyin matasan arewa, masana bangaren tsaro, ta shirya jiya a Gidan Arewa da ke cikin garin Kaduna, a kan matsalar tsaro. Suka farfasa musu gilasan motoci da na tagogin wajen taron. Masu magana da yawun gamaiyar kungiyoyin sun ce wadanda suka kawo musu harin makiyan Arewa da Nijeriya ne.

5. Janar-janar na soja da ya harbu da kwaronabairos zuwa yanzun sakamakon taron Buratai, ya kai ashirin da shida.

6. A jihar Kogi an yi bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi ashirin da daya, da mataimakansu mata ashirin da daya. Taronsu suka yi ba ruwansu da wani abu wai shi kwaronabairos.

7. A jihar Kaduna, gwamnati ta ba da umarnin rufe duka makarantu bayan an kammala karatun gobe Laraba. Manyan makarantu an ce su tsara yadda za su koyar da dalibansu ta intanet, su kuma yara su ci gaba da sauraron koyar da su da ake yi ta rediyo da talabijin wato E-learning. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dau matakin ne saboda kwaronabairos ta dawo. Sai dai ana ta takaddamar wanda ya dawo da ita. Wasu na zargin gwamnan ne da kansa da yake ya fita kasashen waje, ya kawata. Wasu na zargin guje-gujen da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya ne, bakin da suka zo daga kasashen waje suka kawota. Ita kuma gwammati ta ce jama’a ne da ba sa kiyayewa suka kawo ta.

8. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 201 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Kaduna 74 Kaduna 74 Kaduna 74
Legas 53
Katsina 40
Ribas 11
Filato 9
Kwara 6
Bauci
Ogun 2
Taraba 2
Edo 1
Sakkwato 1

Jimillar da suka harbu 73,374
Jimillar da suka warke 66,314
Jimillar da ke jinya 5,863
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,197

9. Malaman jami’a sun ce Gwamnatin Tarayya suke jira ta yi motsi, sai su ma su motsa, yara su samu su ma su matso makaranta.

10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekarar da ke shirin kankama, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

11. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af!
Kare ya ga rawar kura ya ce da kyau.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply