Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 16.01.2021

Taskar Guibi: 16.01.2021

145
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Asabar, biyu ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Jiya ta kasance ranar tunawa da ‘yan mazan jiya, inda a Abuja, Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari, sa manyan mukarraban gwamnatinsa irin su Osinbanjo, zuwa hafsoshin tsaron kasar nan, kowanensu ya dora fure a kabarin dogon yaro. Haka nan a sauran jihohi gwamnonin da manyan mukarrabansu sun dora furen na tunawa da ‘yan mazan jiya da suka kwanta dama. A tarayyar da jihohi bayan dora furen, an saki tantabaru masu alamta zaman lafiya, da harba bindiga, kuma da ma tuni aka kaddamar da tambarin waiwayen na bana, da kuma sanya hannu a rajista.

2. Sojojin da suka yi ritaya, sun yi amfani da wannan dama ta tunawa da ‘yan mazan jiya, wajen gode wa gwamnati, saboda biyansu fansho duk da ba shi da yawa, da neman ta ci gaba da kula da jin dadinsu, da kuma nuna a shirye suke, su taimaka wajen daukar makami don taimaka wa tsaron kasar nan.

3. Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC, ta ce ba ta fa amince a yi amfani da wani magani a matsayin maganin kwaronabairos ba, da gargadin jama’a cewa, magungunan da suke ta sha a matsayin maganinta, na iya jefa rayuwarsu cikin hadari, har ma ga mutuwa.

4. Hukumar ‘Yan Bautar Kasa NYSC da wasunmu masu fassara kan fassarata da Hukumar Yi Wa Kasa Hidima, ta fitar da sunayen wadanda za su yi bautar ko hidimar na rukunin B, tare da bukatarsu, su leka dandalinta na intanet, don duba sunayensu, da jihohin da aka tura kowa.

5. Sojojin Nijeriya sun ce a yanzun kam, babu sauran wani bangare na kasar nan da ke hannun kungiyar Boko Haram ko ISWAP da sauran ire-irensu.

6. A jihar Binuwai, ciwon kwalara ya yi sanadiyyar mutuwar mutum goma sha hudu cikin kankanin lokaci.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

8. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya daukar musu na gyara musu gada, a lokacin yakin neman zabe.

9. Jiya ina fa da alkaluman masu kwarona na shekaranjiya, amma na manta ban sa a labarun na jiya ba. Abin da nake iya tunawa, shi ne babu na jihar Kaduna a na shekaranjiyan. Sabbin da suka harbu na yau ko in ce alkaluman da aka bayar jiya da daddare, mutum 1,867 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 713
Filato 273
Abuja 199
Kaduna 177
Oyo 79
Inugu 58
Ondo 53
Kano 49
Sakkwato 43
Ogun 37
Oshun 37
Nasarawa 36
Ribas 28
Binuwai 24
Delta 24
Neja 24
Gwambe 18
Edo 15
Taraba 12
Bayelsa 10
Ekiti 9
Barno 6
Zamfara 2
Jigawa 1

Jimillar da suka harbu 107,345
Jimillar da suka warke 84,535
Jimillar da ke jinya 21,397
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,413

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya na je sayen gawayin girki. Sai na tarar ya kara tsada, wato naira dubu biyu kowanne buhu. In har za a mun ragi, to za a rage mun naira hamsin kowanne buhu. Sai na tambayi dalilin tsadar. Sai suka ce mun sojoji sun hana shiga daji yanzun. Sojoji sun mike tsaye wajen farautar ‘yan fashin daji, da kidinafas, da sauran miyagun mutane da ke dazukan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply