Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 16.02.2021

Taskar Guibi: 16.02.2021

93
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, hudu ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Fabrairu, shekarar 2021.

1. Labarin da ya fi farin jini jiya shi ne zabar Dafta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Babbar Shugabar Cibiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya wato WTO a takaice. Mace ta farko da aka taba zaba a wannan mukami, ‘yar Afirka ta farko, ‘yar Nijeriya ta farko. Da ma tana ta yin ta farko a abubuwa, misali ita ce ministar kudi ta farko mace, ta yi a zamanin Obasanjo, aka kuma nada ta a gwamnatin Jonathan, wacce ita ce mace ta farko kuma ministar kudi da ta taba samun haka. Shugaban Kasa Buhari, da Shugabannin Majalisun Dokoki su Ahmed Lawan da Gbajabiamila sun nuna farin cikinsu da zabarta.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya tura wasu dakarun ‘yan sanda na musamman da ake jira da INTERVENTION AND STABLIZATION FORCES, Kasuwar Sasa ta jihar Oyo da Yarbawa suka yi wa Hausa rotse don dauki da daidaita lamura.

3. Gwamnonin jihohin Arewa hudu, na Zamfara, da na Kabbi, da na Kano, da Neja, sun yi wa gwamnan jihar Oyo Makinde takakkiya har jihar, su ji dalilin da ya sa Yarbawa ke yawan yi wa Hausawa da ke can rotse.

4. Gwamnonin jihohin Arewa Maso Yamma, sun yo takakkiya zuwa nan Kaduna, inda suka yi taro da hafsoshin tsaro, da mai ba shugaban kasa shawara bangaren tsaro, don yi wa matsalar tsaro da ke addabar yankin taron dangi, su yi koli-koli da ita, su tandara da kasa, sai dai kashi! Sun ce sun so su yi tuya su manta albasa, ba sarakuna ba malamai, saboda haka, kowa ya mayar da akayau dinsa, sai an kara shiri.

5. Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum uku, da kona gidaje a jihar Filato.

6. Za a gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar Kaduna a ranar Asabar 15 ga watan Mayu na wannan shekara.

7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya musu na zai gyara musu gada, a lokacin yakin neman zabe. Sun cika alkawari sun zabe shi, har yana shirin cika shekara uku, a gudanar da sabon zabe, bai gyara musu ba.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Jiya ma hukumar da ke kaso da raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos ta yi wa jihohi kwaron kason kamar shekaranjiya. Shekaranjiya ta raba wa jihohi 520 kawai, jiya kuma 574. Sai dai a rabon na shekaranjiya da na sa jiya na yi kuskure na tsallake na jihar Kaduna, da aka ba ta 21. Ga yadda rabon na jiya ya kasance:

Kwara 98
Legas 81
Edo 59
Ondo 44
Abuja 41
Kano 34
Ogun 33
Kaduna 29
Oshun 28
Inugu 23
Ribas 18
Delta 16
Akwa Ibom 15
Bauci 12
Imo 10
Barno 8
Neja 8
Kabbi 7
Nasarawa 5
Gwambe 3
Ekiti 2.

Jimillar da aka hankada wa Nijeriya zuwa yanzun, kusan shekara daya da soma rabon, 146,928
Kason da aka ware wa wadanda suka warke, 123,009
Kason da aka ware wa matattu 1,761.
Kason da aka kasafta wa majinyata 22,158.

Mu wayi gari lafiya.

Af: Da karfe hudun asubah ta gota da wajen minti goma, sai in ga mutane na ta kiran wayata, wai ba su ga na sako labaru ba. Sai in ta ba su hakuri cewa ina kan rubutawa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply