Assalami alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da uku ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Ministan Lafiya ya yi korafin a yanzun yawan masu zuwa asibiti da lalura ta rashin lafiya ya ragu da rabi. Misali idan mutum dari ke zuwa a da, to a yanzun bai fi mutum hamsin ke zuwa ba.

2. Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, ya umarci dukkan hukumomi da sassansu da ke da nasaba da ma’aikatar tasa, nan da kwana arba’in da biyar su tarkata inasu-ina na shalkwatocinsu su koma Babban Birnin Tarayya Abuja don a samu saukin gudanar da komai musamman a yanzun da aka shiga mawuyacin saboda kwaronabairos.

3. Babban Mai Shari’a na Kasar nan Tanko Muhammad ya umarci dukkan manyan masu shari’a na duka jihohin kasar nan har da Abuja, su hanzarta kammala shari’u da ke gabansu don samun saukin cunkoso a gidajen gyara halinka da ke kasar nan, musamman a yanzun da ake fama da kwaronabairos da kokarin kaucewa yaduwarta.

4. Hukumar EFCC ta mika wa gwamnatin jihar Legas wani katafaren gida da ke Legas, na tsohuwar ministar mai Diezani Alison Madueke da kotu ta kwace ta mallaka wa gwamnatin tarayya, ya zama wajen killace masu jinya ta kwaronabairos.

5. Hukunar Lafiya ta Duniya WHO a takaice, tare da hadin gwiwar wasu jihohin kasar nan, sun dukufa gano maganin kwaronabairos.

5. A duniya bakidaya, wadanda suka harbu da kwaronabsiros sun kusan miliyan hudu da rabi, daga cikinsu dubu dari uku da biyu sun riga mu gidan gaskiya.

6. Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Aminesti Intanashinal ta ce cin zali ne kafa kotunan-tafi-da-gidanka da ake yi a wasu jihohi da ke yanke wa wadanda suka saba wa dokar kulle hukunci daban-daban.

7. A yankin Lamurde da ke jihar Adamawa, an yi wani rikici shigen na kabilanci tsakanin Hausawa/Fulani da wasu kabilu da ke yankin, har da kashe-kashe.

8. Sakamakon yadda makasa, da kidinafas ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a wasu sassan jihar Kaduna, gwamna Nasir El-Rufai ya gana da hukumomin tsaro don gano bakin zaren magance matsalar dayani. Har ila yau a jihar ta Kaduna manyan mukkaraban gwamnatin jihar ke taimaka wa gadin kan iyakokin jihar don hana wadanda suka harbu da kwarona tsallakowa.

9. Malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin an sa su cikin tsarin nan na IPPIS karfi da yaji, da ya sanya albashin da aka biyu su na watan Fabrairu da na Maris an musu kwange ba kadan ba, wasu ma albashin ya makale, wasu an musu gibi, wasu wawulo.

10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata daya kenan suna zaman jiran ariyas, har yau ba amo ba labari.

11. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, akwai mutum 288 sabbi da suka harbu da kwaronabairos a jihohi kamar haka:

Legas 179
Kaduna 20
Katsina 15
Jigawa 15
Barno 13
Ogun 11
Kano 9
Abuja 7
Neja 4
Ekiti 4
Oyo 3
Delta 3
Bauci 3
Kwara 2
Edo 1

Da ke nuna kowacce jiha tana da jimilla kamar haka:

Legas 2278
Kano 761
Abuja 386
Katsina 239
Bauci 210
Barno 204
Jigawa 191
Ogun 145
Kaduna 134
Gwambe124
Sakkwato 112
Edo 93
Oyo 76
Zamfara 73
Kwara 58
Oshun 42
Ribas 33
Yobe 32
Kabbi 31
Nasarawa 29
Delta 25
Adamawa 21
Filato 21
Ekiti 19
Ondo 19
Taraba 17
Akwa Ibom 16
Neja 14
Inugu 12
Ebonyi 9
Imo 7
Bayelsa 6
Binuwai 4
Abiya 2
Anambra 2
Kogi 0
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 5,445
Jimillar wadanda suka warke 1,320
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 171
Jimillar da ke kan jinya 3,954

Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.

Af! Gaskiya talakawan jihar Kaduna na korafin ya kamata Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya mike tsaye, a kan yadda kidinafas ke cin karensu babu babbaka a ciki da wajen garin Kaduna. Suka ce ya kamata idan ya manta a tuna masa, Allah zai tambaye shi.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply