Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 16.06.2020

Taskar Guibi: 16.06.2020

172
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da hudu ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Yuni, na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa a watanni biyar da suka gabata, akwai bayanai da ke nuna an yi fyade guda dari bakwai da goma sha bakwai. Aka danganta karuwar fyaden ga dokar kulle da aka sa jama’a ciki.

2. Kungiyar Amnesty International ta kare hakkin bil’Adama, ta bukaci gwamnatin tarayya ta nuna da gaske take yi wajen magance matsalar tsaro da ke ci gaba da tabarbarewa a arewacin Nijeriya.

3. ‘Yan sanda sun damke wasu daga cikin wadanda suka kai hari Kadisau da ke jihar Katsina, har suka kashe fiye da mutum hamsin da daya.

4. Jami’an tsaro na sibildifes sun damke mutum goma sha daya da ke sayar wa ‘yan kungiyar Boko Haram manfetur da sauran kayayyakin da sukan bukata a jihar Barno.

5. Jami’an tsaro sun damke mutum shida da suke zargi suna da hannu a kisan mutum tara da aka yi a rikicin da ya auku a karamar hukumar Agatu da ke jihar Binuwai.

6. Mutanen kauyuka goma sha shida suka tsere daga kauyukan nasu da ke jihar Katsina zuwa garuruwa daban-daban gudun hijira. Wata ta ce haka suke cunkushe mutum goma sha tara a daki daya, a inda suka samu mafaka.

7. A jihar Zamfara wuraren Dan Sadau wasu mahara sun kashe na kashewa suka kwashi na kwashewa maza da mata ashirin da shida a shekaranjiya lahadi.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

9. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbi wadanda suka harbu da kwaronabairos su 578 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 216
Ribas 103
Oyo 68
Edo 40
Kano 21
Gwambe 20
Abuja 17
Delta 13
Filato 12
Bauci 12
Neja 10
Kabbi 9
Ogun 8
Ondo 8
Abiya 7
Nasarawa 5
Barno 1
Kwara 1
Binuwai 1
Anambara 1

Kowacce jiha tana da jimilla kamar haka:
Legas 7,319
Abuja 1,264
Kano 1,158
Edo 620
Ribas 592
Oyo 575
Ogun 567
Kaduna 446
Barno 439
Gwambe 430
Bauci 422
Katsina 414
Jigawa 317
Delta 280
Nasarawa 177
Abiya 173
Filato 168
Ebonyi 162
Kwara 151
Imo 136
Sakkwato 132
Zamfara 76
Ondo 72
Anambara 66
Kabbi 66
Neja 66
Inugu 57
Yobe 55
Oshun 50
Akwa Ibom 48
Adamawa 42
Binuwai 35
Bayelsa 32
Ekiti 30
Taraba 18
Kogi 3
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 16,658
Jimillar wadanda suka warke 5,349
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 424
Jimillar wadanda suke jinya 10,885

Af! Ana ci gaba da korafi a kan tabarbarewar tsaro a Arewa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply