Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 16.12.2020

Taskar Guibi: 16.12.2020

415
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, daya ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Disamba, na shekarar 2020.

1. Babban Bankin Duniya ya amince wa Nijeriya wani bashi da ta nema, Dala Biliyan Daya da Rabi.

2. Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da shirin nan na daukar matasa su dubu dari bakwai da saba’in da hudu aiki, da ake ta takaddama da karamin ministan kwadago Kiyamo a kai, har sai sun duba sunayen wadanda aka sa za a dauka tukuna.

3. Akwai hauhawar farashin kayan abinci da kashi goma sha takwas da rabi cikin dari a watan jiya.

4. Akwai hauhawar farashin kayayyaki da kashi goma sha biyar ba dan kadan a watan jiya.

5. Da gwamnati da kungiyar kwadago suka sanar da rage farashin mai daga litinin da ta gabata, ana ta korafin masu gidajen man ba su rage kudin ba har yanzun, da korafin da karin kudin aka yi da tuni sun kara, amma da yake ragi ne, sun ki ragewa da sauri

6. An kaddamar da titin dogo na daga Legas zuwa Ibadan, dogon ya fara zirga-zarga da fasinja.

7. Sojoji sun ce sun kama wasu ‘yan bindiga har da makamansu a jiharZamfara.

8. Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace ‘yan makarantar sakandare ta Kankara.

9. Yara goma sha bakwai daga cikin wadanda aka sace a makarantar sakandare ta Kankara sun samu sun subuto zuwa gida.

10. Gwamnatin jihar Zamfara, ta rufe dukkan makarantun kwana da na jeka-ka-dawo da ke kan iyakarta da jihar Kaduna, da jihar Katsina da jihar Sakkwato.

11. Gwamnatin jihar Kano ta rufe dukkan makarantunta.

12. Gwamnatin jihar Jigawa ta rufe dukkan makarantu saboda tsoron kwaronabairos.

13. Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe makarantu da ke jihar daga yau, saboda kwaronabairos.

14. Malaman jami’a sun ce Gwamnatin Tarayya suke jira ta motsa, sai su ma su motsa, yara su motsa a koma makaranta.

15. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na GwamnatinTarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan gobe, da watan jibi, da watan gata, da watan citta, da watan shekaran citta, wato watan Afrilu ke nan, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

16. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jiharKaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Suna ta musu alkawarin hanya, shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

17. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 758 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 305
Legas 152
Kaduna 103
Bauci 44
Gwambe 35
Filato 31
Ribas 17
Sakkwato 15
Kwara 13
Kano 9
Ebonyi 8
Ogun 5
Oshun 5
Oyo 4
Edo 4
Anambara 4
Bayelsa 2
Ekiti 1
Taraba 1
Jimillar da suka harbu 74,132
Jimillar da suka warke 66,494
Jimillar da ke jinya 6,438
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,200

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wani rubutu da na yi ranar 15 ga watan Disamba, na 2013 wato jiya rubutun shekararsa bakwai daidai:

“Babu wadanda nake tausayawa da sanyin nan irin zawarawa da gwauraye. Jiya kusa da ofishina goshin almuru na ji wasu manyan ‘yan mata suna jimamin yadda sanyin nan ke kadawa ba su samu mazan aure ba. Har na tausaya musu na kuma lura wannan yanayi da suke ciki yana da hadarin gaske in ba sun hadiye kwadayinsu na bukatar namiji ba a daidai wannan lokaci. To maza a daure a aure su don Allah. Ku kuma matan ku daina hange-hange da rainin arziki aure bautar Ubangiji ne. Ban mantawa a shekarar 2006 na taya wata bazawara sai ta mun kallon biyu-ahu ta ce me na sama ya ci ya bai wa na kasa? Na ba ta hakuri. Tana nan har yanzun ba mijin aure ga shekaru sun soma tsofar da ita. Iri-irinsu na nan birjik”

Sai dai ranar da na yi rubutun, wasu masu hada husuma, suka tsegunta wa wata da muka taba yin haka da ita, suka ce ga ni can ina zaginta a fesbuk. Ta kira ni a waya tana ta fada, tana nanata cewa “Eh na ce bana sonka me na kasa ya ci har ya ishe shi ya ba na sama?” Ina ta ba ta hakuri saboda munafukan da suka hada husumar, sun san ta yi mun wani abin alheri a lokacin da bai kamata a ce ga shi ina yi da ita a fesbuk ba. Na rantse ba da ita nake ba, ta ce atabau da ita nake.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply