Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 17.05.2020

Taskar Guibi: 17.05.2020

280
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da hudu ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Mayu, na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban Kasar Guinea Bissau/Gini Bisau Embalo, ya je fadar shugaban kasa, ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakon shugaban kasar Madagaskar na maganin kwaronabairos da Madagaskar ta ba Nijeriya kyauta. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ba za a soma amfani da maganin ba tukuna, har sai an tura shi ga bangarori daban-daban na kasar nan, don gwada ingacinsa.

2. An raba naira tiriliyan dari shida da shida, da biliyan dari da casa’in da shida a tsakanin gwamnatin tarayya, da jihohi, da kananan hukumomi. Gwamnatin tarayya ta ja naira tiriliyan dari da sittin da tara, da biliyan dari takwas da talatin da daya. Sai jihohi da suka ja naira tiriliyan tamanin da shida, da biliyan dari da arba’in. Kananan hukumomi suka ja tiriliyan sittin da shida, da biliyan dari hudu da goma sha daya. Da ke nuna in an yi sa’a a samu dilin-dilin kafin Sallah, da ta rage kwana biyar ko shida.

3. Gwamnonin jihohin Barno da Bauci sun sa a hanzarta biyan ma’aikata har da ‘yan fansho albashi da fansho na wannan watan na Mayu da muke ciki kafin Sallah.

4. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nemi gafarar mutanen jihar Kaduna saboda kulle su da ya yi a gida saboda tsoron kada su harbu da kwaronabairos, da ya ce da ta harbe shi bai ji da kyau ba.

5. Mutane arba’in da biyar suka riga mu gidan gaskiya a jihar Bauci sakamakon harbuwa da cutar Lasafiba da ake tuhumar bera ke haddasata.

6. Sojojin sama na Nijeriya sun ce sun kai wa ‘yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa hare-hare ta sama, suka kashe su da dama.

7. Malaman kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tatayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata daya ke nan suna zaman dirshan na jiran ariyas dinsu, har yau ba amo ba labari, wasunsu ma har yau dilin-dilinsu na wasu watannin baya, shiru.

8. Wasu daga cikin malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin har yau ba su ga dilin-dilin na watan Fabrairu da Maris da Baba Buhari ya ce a hanzarta biyansu ba. Suka ce tabbas an biya amma kalilan daga cikinsu aka biya, wasu kuma aka ki biyansu.

9. Jihohin kasar nan da ke ba da damar a fita daga kulle a je masallaci da sauran wuraren ibada na ci gaba da karuwa.

10. Kasar Italiya za ta dage dokar hana tafiye-tafiye.

11. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 176 ne a jihohi kamar haka:

Legas 95
Oyo 30
Abuja 11
Neja 8
Barno 8
Jigawa 6
Kaduna 4
Anambra 3
Edo 2
Ribas 2
Nasarawa 2
Bauci 2
Binuwai 1
Zamfara 1

Jimillar wadanda suka harbu 5,621
Jimillar wadanda suka warke 1,472
Jimillat wadanda suka riga mu gidan gaskiya 176.
Jimillar wadanda ke jinya 3,973.

Domin ganin adadin da kowacce jiha ke da shi sai a leka dandalin hukumar yaki da yaduwar miyagun cututtuka ta kasa da ke intanet.

Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.

Af! Korafe-korafe na ci gaba da yaduwa a kan yadda har yau Baba Buhari ya kasa kare talakansa daga makasa, da kidinafas, MUSAMMAN a jiharsa ta Katsina, da jihar Kaduna.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply