Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 17.12.2020

Taskar Guibi: 17.12.2020

427
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, biyu ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Disamba, na 2020.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin hanzarta bude kan iyakoki na tudu na kasar nan guda hudu, sauran kuma a bude su ranar talatin da daya ga watan nan. Wadanda ya ce a bude su yanzu-yanzun su ne kan iyakar Seme, da ke Kudu Maso Yammacin kasar nan, sai Illela da ke Arewa Maso Yammacin Kasar nan, sai Maigatari da ke Arewa Maso Yammacin Kasar nan, sai Mfuni da ke Kudu Maso Kudancin Kasar nan.

2. Majalisar Dattawa ta dage amincewa da kasafin kudi na 2021 har sai Litinin mai zuwa, saboda wata sabuwar bukata da bangaren zartaswa ya mika mata a baya-bayan nan.

3. Majalisar Wakilai ta nemi a kara wa’adin mako biyu da aka ba ‘yan Nijeriya su je su hada rajistar layinsu na waya da lambarsu ta shaidar dan kasa cikin mako biyu ko a dodewa mutum layi. Majalisar ta nemi a kara ya kai mako goma.

4. Kotun daukaka kara ta soke hukuncin da mai shari’a Abang ya yanke wa Metuh na daurin shekara bakwai saboda zargin ya karbi wata naira miliyan dari hudu daga hannun Dasuki a zamanin Jonathan. Kotun ta ce mai shari’a Abang ya yi son kai a shari’ar, saboda haka kotun daukaka kara ta soke hukuncin, ta nemi a ba wani mai shari’an don gudanar da shari’a sabuwa a kan Metuh.

5. Gwamna Bello Masari ya ce yara da aka sace suna dajin Zamfara, kuma a maganar da aka yi da wadanda suka sace su, sun kira waya cewa kudi suke so, kuma ba sa so jirage na damunsu da shawagi. Masari ya ce tun wannan ba su sake kiran waya ba.

6. Gwamna Zulum ya je kasar Cadi ya gana da Idris Derbi shugaban kasar, a kan yadda za a dawo da ‘yan Nijeriya, iyalai fiye da dubu hamsin, da suka gudun can gudun hijira, sakamakon harin Boko Haram.

7. ‘Yan Nijeriya da ke gudun hijira a Nijar, fiye da hansin kungiyar Boko Haram ta bi su har can ta kashe.

8. BBC Hausa ta ba da rahoton wasu ‘yan Bindiga na ci gaba da kashe mutane har da kona su da motocinsu a yankin Dandume da ke jihar Katsina.

9. A jihar Binuwai wasu sun kashe wani lauya, da matarsa da wani. Ortom na jihar da ke zargin Fulani ne suka aikata, bai kai mako guda ba ya zargi Fulanin da kashe wasu mutum hudu a jihar.

10. A jihar Kaduna, wasu kidinafas sun tare hanyar Abuja, sun yi daji da wasu da ke cikin wasu motoci uku.

11. Wasu bayanai da ke ta karakaina a soshiyal midiya, na cewa Aisha Buhari ta zabi ta yi zamanta a Dubai saboda matsalar tsaro.

12. Malaman jami’a sun ce GwamnatinTarayya ce har yanzun ba ta motsa ba, shi ya sa su ma ba su motsa, sun janye yajin aikin don yara su motsa zuwa makaranta ba.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin sun kusan cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

14. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo ga shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya gyara musu gadar da ya dauki alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

15. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 930 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 279
Abuja 179
Filato 62
Kaduna 54
Kano 52
Katsina 52
Imo 42
Jigawa 42
Ribas 38
Kwara 30
Nasarawa 19
Yobe 15
Ogun 13
Barno 10
Oyo 9
Neja 9
Ebonyi 6
Edo 5
Taraba 4
Sakkwato 2
Kuros Ribas 2

**Wasu jihohin ma anko suke yi da juna a alkaluman.

Jimillar da suka harbu 74,062
Jimillar da suka warke 66,775
Jimillar da ke jinya 7,087
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,200.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina shawagi a fesbuk, sai na yi kicibis da wannan korafi sai dai cikin harshen Ingilishi ne, kuma na cire sakin layi na farko saboda ZARGI ne:

“……………………………………………..
The FG reached an agreement with ASUU that every outstanding financial issue would be taken care of by the 9th and 11th of December 2020 respectively for withheld salaries and allowances so that universities would reopen.

Consequently, ASUU slated their congresses for the 15th of December to vote in favour of suspending the strike owing to the belief that by then, the FG would have fulfilled its promise.

On arriving at these congress venues on the 15th, four days after the lapse of the deadline FG gave itself, ASUU members were informed that the FG said it couldn’t fulfill the promises because it was saving for the second wave of COVID-19.

Saving for the 2nd wave of COVID-19 while students and their teachers are in the 9th wave already?

And in all these, to some of the advocates of justice and fairness, ASUU is the one who’s not willing to end this strike”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply