Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 18.10.2020

Taskar Guibi: 18.10.2020

352
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, daya ga watan Rabi’ul Auwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha takwas ga watan Oktoba, shekarar 2020.

1. Aisha Buhari ta shiga zanga-zangar lumana ta neman gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro a jihohin Arewa.

2. Matasan Arewa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga ta lumana a jihohin Arewa, ta neman gwamnati ta kawo karshen kidinafin, da kashe-kashe, da satar dabbobi da sauran matsaloli na tsaro da ke addabar Arewa.

3. Gwamna Zulum na jihar Barno ya ayyana gobe litinin a matsayin ranar azumi da addu’o’i a fadin jihar.

4. A jihar Kano ambaliya ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 54, da salwantar gida dubu talatin, da dari uku da hamsin da shida.

5. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 113, a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 37
Kaduna 16
Ogun 11
Filato 11
Taraba 8
Ribas 7
Abuja 6
Inugu 4
Neja 4
Edo 3
Delta 2
Imo 2
Binuwai 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 61,307
Jimillar da suka warke 56,557
Jimillar da ke jinya 3,627
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,123

6. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata takwas ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau ma ta marigayi Alhaji Mamman Shata.

Mu gargadi mai gina ramin mugunta.
In za ka gina ramin mugunta, gina shi daidai kai don watakil kai ka fada mu gargadi mai gina ramin mugunta.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply