Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 19.11.2020

Taskar Guibi: 19.11.2020

362
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis uku ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha tara ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1 Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 236 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 142
Ogun 19
Kaduna 15
Abuja 14
Imo 14
Ribas 14
Filato 6
Katsina 3
Ekiti 2
Jigawa 2
Oyo 2
Kuros Ribas 1
Kano 1
Taraba 1

Jimillar da suka harbu 65,693
Jimillar da suka warke 61,457
Jimillar da ke jinya 3068
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,168

2. A yanzun Nefa sun rage yawan awoyin da suke ba mu wuta. Karfe 12 na dare na yi za a dauke, sai karfe uku da rabi da minti takwas na goshin asubah kamar yadda suka yi lokacin da nake zaune nake wannan rubutu, su dawo da ita. Can wuraren karfe takwas ko tara na safe su dauke, sai kuma, can wuraren karfe biyu ko uku su dawo da ita. In ba a yi sa’a ba karfe biyar su dauke, sai kuma goshin magriba su dawo da ita. Sannan mu kwana uku da wuta, kwana daya babu. Ga wutar ba karfi, da in kana da mitar iya-kudinka-iya-shagalinka mitar ba ta nunawa saboda wutar ba karfi.

3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce in Allah Yarda ba za a sake yin makamanciyar zanga-zangar tir da halayen ‘yan sanda ba.

4. ‘Yan sanda masu mukamin ASP su goma sha biyu kidinafas suka yi kidinafin a kan hanyarsu ta Barno zuwa Zamfara, inda kidinafas din suka nemi sai an ba su naira dubu dari takwas kowanne dan sanda. Wato naira dubu dari takwas sau goma sha biyu ke nan.

5. Kidinafas da suka yi kidinafin daliban jami’ar Ahmadu Bello Zariya, su tara a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun nemi sai an ba su jimillar naira miliyan 270 kafin su sako yaran.

6. Da alamu sai shekara mai zuwa, Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tattaunawa da malaman jami’a a kan yajin aikin da suke yi. Daliban jami’a ba batun komawa ke nan yanzun.

7. An raba naira biliyan arba’in da ‘yan kai tsakanin Gwamatin Tarayya, da Gwamnatocin Jihohi, da Gwamnatocin Kananan Hukumomi na watan Oktoba, da ke nuna an kusan soma jin dilin-dilin ga masu samu da wuri ke nan.

8. Kotu ta ba da umarnin a kamo mata Maina. Mainan nan fa da ake ta tirka-tirka da shi a kan zargin wasu kudade na fansho.

9. Dan autan Fela, Seun ya farfado da jam’iyyar mahafinsa ta Movement of the People.

10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

11. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Da yake a karshen rubutuna na jiya, na tabo batun kamen masu takardun mota da suka kare aiki, da wadanda lasisinsu ya kare aiki, da masu tsohuwar lamba ire-irena, da aka soma a fadin jihar Kaduba, wani ya yi tsokaci kamar haka:

“Mal. Guibi, ni Ina ganin kafin a Kama motocin mutane dake da tsohuwar lamba, kamata ya yi su fara da motocin gwamnati. Domin kuwa kashi 99 cikin 100 na motocin gwamnatin Jihar Kadunan, duk su na dauke da tsofaffin lambobi ne. Na biyu, ba Kotu ta hana tilastawa ‘yan Kasa sayen wannan lambar ba, aka ce kowa ya na da ikon amfani da lambarsa? Na uku, sayar da lambar ba aikin Road Safety ba ne? Me ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta karbe wannan aikin daga FRSC? Ita gwamnatin Tarayya ba ta bukatar kudaden shiga ne?”

Wani kuma ya kara da cewa ya za a yi da masu motoci na wasu jihohi da ke bi ta Kaduna su wuce, da su a johinsu ba a hana amfani da tsohuwar lambarba?

Wani kuma ya ce me ya sa ita gwamatin jihar Kaduna ta fi damuwa da abin da za ta samu a hannun jama’a ba kare su daga kidinafas da makasa da barayin dabbobi da ke cin karensu babu babbaka, musamman a ‘yan kwanakin nan a jihar Kaduna ba?

Ni dai na yi nan

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply