Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 20.01.2021

Taskar Guibi: 20.01.2021

134
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Laraba, ta Bawa ranar samu, 6 ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Yau wa’adin da Pantami ya bayar na kowa ya je ya yi rajistar shaidar dan kasa, da hade lambar shaidarsa ta dan kasa da layinsa na waya ke karewa. Inda ya ce duk wanda bai yi ba za a dode layinsa. Zuwa jiya hukumar ta Pantami, ta ce kamfanonin sadarwa na waya, sun mika mata layin mutum miliyan arba’in da takwas, da dubu dari takwas (47.8) da suka hade lambobinsu da layukansu. Mutum nawa ne ma a Nijeriya? Layukan waya nawa ne ma a hannun jama’a? Sai a cire miliyan 47.8, a ga mutum nawa suka yi saura? Layukan waya nawa suka yi saura? Mutum nawa za a dode wa layi ke nan?

2. Kwamitin Shugaban Kasa a kan kwaronabairos PTF a takaice, ya ce a cikin kowanne dan Nijeriya biyar, daya a cikinsu ya harbu da kwaronabairos.

3. Gwamnatin Tarayya, ta ce za ta yi wa mutum 450 a kowacce karamar hukuma ta kasar nan guda 774, gwajin kwaronabairos.

4. Gwamnatin Tarayya, ta ware naira biliyan goma, domin samar da rigakafin kwaronabairos, samfurin Nijeriya.

5. Gwamnatin Tarayya, ta ce ba sai an yi wa dalibai da ke komawa makaranta gwajin kwaronabairos ba, amma za a dinga gwada zafin jikinsu.

6. Gwamnatin Tarayya, ta yi tanadin wajen ajiye alluran rigakafin kwaronabairos gudu dubu dari hudu samfurin PFIZER, a Abuja, da za a soma da kawo guda dubu dari zuwa karshen watan nan.

7. Gwamna Yahya Bello na jihar Kogi, ya nuna akwai matsala tattare da alluran rigakafin kwarona da ake kokarin yi wa jama’a, sai dai wata ruwayar na cewa jam’iyyarsa ta APC na ja masa kunnen kada ya bata SHOW.

8. Ranar 25 ga wannan watan za a koma makaranta a jihar Katsina.

9. Gwamnatin jihar Kano ta umarci ma’aikata su daina zuwa wajen aiki, su dinga gudanar da aikin daga gida, da umartar jama’a su kaurace wa gidan kallon kwallo, da shagulgula, saboda yadda kwarona ke ci gaba da yaduwa a jihar. Sai dai hanin bai shafi makarantun da ke jihar ba.

10. Yau gwamnonin Nijeriya za su yi taro a kan kwaronabairos.

11. Hukumar tara kudaden shiga na cikin gida ta tarayya, FIRS, ta tara naira tiriliyan 4.9, a shekarar 2020, kashi 98 na jimillar da ta yi hasashen tarawa a shekarar.

12. Wata gobara ta auku a kasuwar jihar Sakkwato.

13. Wani bayani na nuna akwai a kalla al’umomi tara da ke yankin kananan hukumomin Shiroro da Rafi a jihar Neja, da ke hannun ‘yan bindiga.

14. Kidinafas sun yi kidinafin Farfesa Aliyu Mohamned, suka kashe dansa da wasu mutum uku, a karamar hukumar Zariya, da ta Giwa da ke jihar Kaduna.

15. A Kafanchan da ke jihar Kaduna, takaddama ce a kan rashin wutar lantarki, har ta yi sanadiyyar harbin wani dalibi.

16. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

17. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dau alkawarin gyara musu a lokacin yakin neman zabe.

18. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos, mutum 1,301, a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 551
Abuja 209
Oyo 83
Filato 65
Kaduna 64
Inugu 61
Ribas 44
Ondo 39
Binuwai 37
Akwa Ibom 31
Kano 19
Delta 18
Gwambe 18
Ogun 16
Edo 15
Kabbi 10
Ebonyi 9
Jigawa 4
Oshun 3
Zamfara 3
Barno 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 113,305
Jimillar da suka warke 91,200
Jimillar da ke jinya 20,641
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,464

19. Yau za a rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka, na 46.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Af!! Af!!!

Idan an ji ni shiru, an dode mun layukana na waya. Don saboda tsoron kwarona, ban iya zuwa na shiga cunkoson jama’a masu rajistar shaidar dan kasa ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply