Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 20.02.2021

Taskar Guibi: 20.02.2021

46
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Asabar, takwas ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Fabrairu, shekarar 2021.

1. Gwamnatin Tarayya za ta sa wa gidaje miliyan shida lantarki mai amfani da hasken rana cikin watanni uku masu zuwa. Sannan hukumar da ke sanya ido a kan batun lantarki ta kasa NERC, ta ce kamfanonin raba wutar lantarki da ake kira DISCOs, za su biya kudi shigen na tara, saboda kin karbar wutar daga inda ake ba su ita.

2. Kwamitin nan da ke kaso da raba wa gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi kudaden da aka samu na shiga duk wata, ya raba musu naira biliyan 640 da ‘yan kai na watan Janairu, da ke nuni da an kusan jin dilin-dilin na watan Fabrairu.

3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Abubakar Ahmed Audi a matsayin sabon babban shugaban hukumar tsaron farin kaya NSCDC, biyo bayan ritayar da tsohon shugaban hukumar ya yi.

4. Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta kaddamar da yajin aiki a jihohi goma sha takwas na kasar nan, da har yau ba su soma biyan ma’aikatansu sabon albashi mafi karanci wato Minimum Wage ba.

5. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi da aka dade da biyan sauran ma’aikata.

6. Gwamnan jihar Sakkwato ya karbi daruruwan ‘yan asalin jihar da suka tsero daga Ibadan ta jihar Oyo sakamakon rotsen da Yarbawa suka yi wa Hausawa a kasuwar Sasa.

7. A Abuja an bankado wata makaranta da ake koyar da damfara ta hanyar intanet wato Internet Fraudsters Academy.

8. A jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta sanar da cewa jibi Litinin, sauran ‘yan makaranta, na naziri, da firamare da sakandare da Islamiyya da aka ce su tsahirta komawa makaranta da farko, za su koma makaranta.

9. Gwamnan jihar Neja, Bello ya ce a kokarin da yake yi na tabbatar da tsaro a jihar, har jirage marasa matuka ya sayo, matsalar ita ce samun izini kafin soma amfani da su.

10. Shek Dafta Gumi, ya kutsa dajin da kidinafas suke a jihar Neja, ya musu wa’azi da raba musu littafai na koyar da addini, da bayanin nan gaba kadan za a sako wadanda aka yi kidinafin, da rokon gwamnati ta yafe wa wadanda ke neman tuba a cikin kidinafas din.

11. Gwamnan jihar Bauci Bala Mohammed, ya ce kalaman da ya yi na dole ka ga bafulatani na kiwo da AK47 don kare kansa, FIGURE OF SPEECH ya yi.

12. Wasu bayanai na nuna ‘yan Boko Haram sun karbe Barte da ke Arewacin jihar Barno.

13. A yankin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, ana zargin da wuya gari ya waye a yini kidinafas ba su je yankin, da safe ko da rana ko da daddare sun yi kidinafin ba. Na baya-bayan nan sun yi kidinafin shugaban al’umar Gwari a fadama, bayan sun dauki wata matar aure da diyarta.

14. Kwamitin bincike na shari’a a kan cin zali da ake zargin ‘yan sanda, da ke zama a Legas, ya yanke hukunci biyan naira miliyan goma ga iyalan wata Abayomi da wani dan sanda ya bindige ta mutu ya ce tsautsayi ne, za kuma a hukunta shi, da daukar nauyin karatun ‘ya’yan da ta bari. Sai wata naira miliyan goma ga wata Olugbodi, ita ma wani dan sanda ne ya ci zalinta da bindiga.

15. Ana ci gaba da ankarar da mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, cewa wasu ‘yan siyasan yankin, masu neman tazarce, sun buga fostarsu da hoton wata gada, da suke cewa gadar Guibi ce suka gyara, alhali gadar na nan har yanzun ba su gyara ta ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina ta leka dandalin da ake kaso da raba wa jihohi alkaluman kwarona, har zuwa kammala wannan rubutu da karfe hudu na asubah, ban ga sun fitar da alkaluman jiya ba. Sannan Allah Ya yi wa abokin aikinmu a DITVAlheri rediyo, kuma dalibina a kwalejin foliteknik ta Kaduna da ke karatun aikin jarida, Adamu Mamman rasuwa, jiya a asibitin sojoji na fotifo da ke cikin garin Kaduna. Allah Ya jikansa, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply