Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21.01.2021

Taskar Guibi: 21.01.2021

145
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, bakwai ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Janairu, na 2021.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon shugaban Amurka Joe Biden, da mataimakiyarsa Kamala Harris murnar rantsar da su, da musu fatan alheri, da ci gaba da tafiya tare, da hadin kai da Nijeriya.

2. Taron Majalisar Zartaswa ya amince da kudirin kara wa malaman makaranta shekarun aiki daga shekara 35 zuwa 40, ko shekarun haihuwa daga 60 zuwa 65 kafin ritaya. Majalisar Zartaswar za ta aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa don amincewa da mayar da shi doka.

3. Fadar Shugaban Kasa ta mayar wa da gwamnan Ondo Akeredolu martanin umarnin da ya ba fulani makiyaya, na su bar dazukan jihar. Fadar shugaban kasa ta ce masa ya kamata, ya iya tantance da bambance masu laifi, daga wadanda ba masu laifi ba ne. Ba dukkansu ya tara su ya musu kudin goro ba.

4. Masu kokarin samun lambar shaidar dan kasa sun fusata, sun yi bore a Kubwa da ke yankin Abuja, saboda zargin masu yin aikin rajistar, na nuna son kai, da karba kudi.

5. Gwamnatin Tarayya, ta ce ba ta fa amince wa wani dan sintiri ko Amotekun ya rike makamai ba.

6. Nijeriya ce ta hudu, cikin manyan kasashen da ke sayar wa da Indiya danyen mai.

7. Kotu ta sa daya ga watan gobe, ta zama ranar duba batun ba da belin Abdulrasheed Maina, saboba batun lafiyarsa.

8. Malaman Jami’a sun ci gaba da korafin, albashin wata biyu kawai suka gani, sannan, sauran alkawuran ma, ba wanda gwamnatin tarayya ta cika musu. Da ke nuna alamun za su koma yajin aiki a watan gobe.

9. Ma’aikatan Kwalejojin Foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

10. Dafta Shek Gumi ya ci gaba da kutsawa dazukan da kidinafas suke yana musu wa’azi, inda na baya-bayan nan shi ne dajin Kidandan da ya gitta Giwa da Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, inda kwamandojin fulani kidinafas su wajen dubu daya, suka nuna sun tuba da alkawarin sun daina.

11. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawari a lokacin yakin neman zabe. Ga shi wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.

12. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos, mutum 1,386 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 476
Ribas 163
Abuja 116
Kaduna 114
Oyo 68
Filato 62
Ogun 56
Imo 55
Oshun 55
Edo 51
Anambara 50
Kwara 44
Kano 17
Ebonyi 14
Kuros Ribas 10
Delta 10
Jigawa 8
Bayelsa 6
Ekiti 6
Barno 2
Taraba 2
Zamfara 1

Jimillar da suka harbu 114,961
Jimillar da suka warke 92,336
Jimillar da ke jinya 21,147
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,478

13. Jiya wuraren karfe goma sha biyu na rana sauran wasu mintoci agogon Amurka, aka rantsar da Joe Biden ya zama shugaban Amurka, kuma mafi tsufa a shekaru. Da mataimakiyarsa, mace ta farko, da ta taba zama mataimakiyar shugaban kasar Amurka. Saboda kwaronabairos, tuta guda dubu dari biyu aka sa a wajen rantsarwar, da ke wakiltar Amurkawa da ba su iya halarta ba. Trump ya ki halartar wajen rantsarwar amma mataimakinsa ya je. An nuna mutanen Hindu na ta rawa da murna saboda Kamala Harris jininsu ce. Ta kuma debo jinin mutanen Jamaika.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ai kuwa shiru ba a rufe layin nawa ba. Ko dai Pantami ya manta ne?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply