Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21.02.2021

Taskar Guibi: 21.02.2021

98
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, tara ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Fabrairu, na shekarar 2021.

1. Ministar harkokin wajen kasar nan Goeffrey Onyeama, ya ce Shugaban Kasar Binin ya ce su fa a shirye suke, su hade da kasar nan ta zama guda daya, su zama jihar Nijeriya ta talatin da bakwai.

2. Sojojin Nijeriya sun ce sun yi nasarar kwato wata katuwar gonar Shekau a kungurmin dajin Sambisa.

3. Tsohon hafsan hafsoshin mayakan kasa na kasar nan kuma jakadan Nijeriya a yanzun Tukur Buratai, ya ce sai Nijeriya ta kai shekara ashirin tana fama da matsalar tsaron da ke addabarta kafin ta iya maganceta.

4. Can na ga zanen wasu hotuna guda biyu a fesbuk da Bulama wani wani fitaccen mai zanen barkwanci ya yi na ta karakaina. Daya na nuna ‘yan fashin daji su biyu zaune da manyan makamai. Daya na kuka, dayan na ba shi hakuri. Mai kukan na cewa yana mamakin yadda ministan tsaro ne ya raina irin makaman da ‘yan fashin dajin ke da shi, da har zai ba talakawa shawarar su dinga daukar wuka, da sanda, suna tunkararsu idan sun kai musu farmaki.
Zane na biyu kuwa yana nuna wani kidinafa ne yana cewa su fa a daji suka kwashi ‘yan makarantar Kagara, ba a makaranta ba. Ya ce inda suka je suka kwashi yaran bai kama da makaranta ba.

5. Ana ci gaba da ankarar da mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, cewa wasu ‘yan siyasan yankin da ke neman ta-zarce, sun buga fostarsu, da hotonsu da hoton wata gada, suna yakin neman zabe cewa gadar Guibi ce suka gyara, alhali gadar na nan har yanzun ba su je sun gyarata ba.

6. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka dade da biyan sauran ma’aikata, su har yanzun shiru.

7. Jiya na bayyana cewa ina ta lekawa dandalin masu raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos, ban ga sun sa na shekaranjiya ba. Kafin in fara wannan rubutu wuraren karfe uku da rabi na dare wato goshin Asubahin nan, na leka, na ga sun raba 662 na shekaranjiya. Na jiya kuma sun raba 645 kamar haka:

Legas 282
Ogun 72
Abuja 50
Kaduna 33
Oshun 24
Imo 23
Abiya 21
Barno 18
Oyo 17
Edo 15
Nasarawa 15
Taraba 14
Ekiti 11
Ondo 11
Filato 11
Kano 10
Ribas 7
Delta 5
Bauci 3
Jigawa 3

Zuwa yanzun an hankada wa Nijeriya 151,553
Aka cire 128, 005 a matsayin wadanda suka warke. Aka cire 1,831 a matsayin matattu. Abin da ya yi saura a matsayin majinyata.

8. Gwamnati ta ce ba za ta biya ko taro, kudin fanso ‘yan makarantar Kagara ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A ranar 20 ga watan Fabrairu, na shekarar 2013, jiya shekara takwas (8) daidai, na yi wannan rubutu:

“Da safe na ji shugaban kasar Faransa yana ta fada kamar zai yi hauka saboda sace wasu ‘yan kasar Faransa da aka yi a kasar Kamaru, da aka ce bayan an sace su an tsallako da su Nijeriya, har ma ya yi zargin ‘yan boko haram ne suka sace su. Abin da na yi tunani shi ne an taba sace wani talakan Nijeriya shugaban kasa ya kidime kuwa? Talakawa da ‘ya’yansu nawa aka sace aka kai su gidan yankan kai shugaban kasa ya yi magana? Ko kuwa sai satar dukiyar talaka aka iya shi kansa talakan in ya yi wasa a sace shi a yi tsafi da shi?”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply