Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21.06.2020

Taskar Guibi: 21.06.2020

95
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da tara ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Yuni na shekarar 2020.

1. Wasu matasa a jihar Kaduna sun bi sawun masu zanga-zangar lumana a kan matsalar tsaro a arewa. Masu zanga-zangar na Kaduna, sun mika sakonsu na neman a kawo karshen kashe-kashen da bukatar a sauya manyan hafsoshin tsaron kasar nan.

2. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu da ke yankin karamar hukukar Batsari, suka kashe mutum bakwai.

3. Wasu shugabannin APC a mazabar Oshiomhole sun ce sun dage dakatarwar da aka masa, sai dai shugaban jam’iyyar na mazabar ya ce ba su dage dakatarwar da suka masa ba. Dakatarwar na nan wacce ita ta sa kotuna suka dakatar da shi daga shugabancin jam’iyyar a kasa bakidaya.

4. Wadanda suka harbu da kwaronbairos a kasar Burazil sun haura miliyan daya.

5. An cire limamin masallacin juma’a na ‘yan lilo da ke Tudun Wadar Kaduna saboda saba wa dokar da gwamnatin jihar Kaduna ta gindaya a kan yadda ya kamata a gudanar da Sallar juma’a a sahu.

6. Jiya gabadaya sun hanu mu wutar lantarki sai cikin dare suka kawo ta.

7. ‘Yan majalisar dokoki ta jihar Gwambe su shida suka warke daga kwaronabairos.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyu har da wasu kwanaki suna jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairu na wannan shekarar.

9. Masu motoci da ke cikin garin Kaduna, na ci gaba da korafi a kan tukin ganganci na ‘yan keke-nafef. Suka ce a da suna tausaya musu idan sun shiga hannun ‘yan sanda. Suka ce amma a yanzun in an kama su, sai su yi ta farin cikin kama su.

10. Likitoci a kasar Zimbabwe sun soma yajin aiki na sai dai a dinga biyansu albashi da alawus da dala ba da kudin kasar ba, saboda darajar kudin kasar ta fadi kasa warwas. Na kuma lura su a Zimbabwe suna da MINISTER OF WEALTH ne maimakon MINISTER OF FINANCE da muke da a nan Nijeriya. Wancan DUKIYA wannan KUDI.

11. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 661 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 230
Ribas 127
Delta 83
Abuja 60
Oyo 51
Edo 31
Kaduna 25
Filato 13
Ondo 6
Nasarawa 3
Ekiti 2
Kano 2
Barno 1

Jimillar wadanda suka harbu a kasar nan 19,808
Jimillar wadanda suka warke 6,718
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 506
Wadanda ke jinya 12,584

Mu wayi gari lafiya.

Af! Akwai wani shiri da na ji ake yi cikin dare zuwa da safe a sabon gidan rediyon BERKETE da ke cikin garin Kaduna, da ‘yan mata da zawarawa da maza samari ko magidanta kan kira su ce suna bukatar aure, take a hada su. Abin da ya ba ni mamaki shi ne yadda yara ‘yan mata, daga shekara sha takwas, zuwa sha tara, zuwa ashirin, da ashirin da daya zuwa da biyu ke kiran waya suna nuna su fa aure kawai suke so. Baro-baro ba boyo. ‘yan mata fa rututu. Shi ne nake cewa anya wannan ba wani kalubale ba ne ga mu iyaye da ke nacewa sai diyarmu ta digire ko kammala karatu kaza sannan mu mata aure kuwa? Anya mu iyaye ba ma shiga hakkin diyanmu mata da ke kosawa su yi aure kuwa?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply