Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21.09.2020

Taskar Guibi: 21.09.2020

312
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, uku ga watan Safar shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Jiya Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris 1936 – 2020 rasuwa bayan wata jinya a asibitin sojoji na fotifo da ke nan Kaduna. Sarkin Zazzau mai shekara 84 a duniya shi ne sarki na goma sha takwas a jerinsu na fulani bangaren Malam Musa da suka soma sarauta a 1804. Shekara 45 Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris ya yi yana sarauta. Jiya aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

2. Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da jibi laraba 23 ga watan nan a matsayin ranar hutu a jihar Kaduna, don zaman makoki da addu’ar rasuwar Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Kaduna Alhaji Dafta Shehu Idris da Allah Ya yi wa rasuwa jiya.

3. Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Gambari da ya jagoranci mukarraban gwamnatin tarayya da suka wakilci shugaban kasa Buhari wajen jana’izar Mai Martaba Sarkin Zazzau, ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi.

4. Manyan ma’aikata, da sarakuna da ‘yan kasuwa manya da kanana, da talakawa da idon gari, da ‘yan uwa da abokan arziki na ci gaba da tururuwa zuwa gaisuwar ta’aziyyar rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris.

5. Gwamna Obaseki na jam’iyyar PDP shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka yi shekaranjiya, ya lika Ize-Iyamu na jam’iyyar APC da kasa da kuri’a dubu dari uku da bakwai, da guda dari tara da casa’in da biyar. Iyamu ya samu kuri’a dubu dari biyu da ashirin da uku, da dari shida da goma sha tara. Tuni Obaseki ya gode wa Shugaban Kasa Buhari da ya yi tsayin daka wajen tabbatar da an yi zabe na gaskiya, har ma Shugaban Kasan ya taya Obaseki murnar nasarar da ya samu.

6. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 97 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 46
Kwara 12
Ribas 11
Adamawa 4
Neja 4
Ogun 4
Oshun 4
Ekiti 3
Imo 3
Kaduna 3
Filato 2
Abuja 1

Jimillar da suka harbu 57,242
Jimillar da suka warke 48,569
Jimillar da ke jinya 7,575
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,098

7. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

8. ‘Yan bindiga sun je Gobirawar Chali da ke yankin karamar hukunar Maru ta jihar Zamfara, sun tafi da mutane kusan hamsin, mutum dubu uku da dari biyar suka tsere daga gidajensu. Haka nan a Kasuwar Magani da ke jihar Kaduna wasu kidinafas sun yi kidinafin wasu mutane.

9. Ma’aikatan lafiya da ke yajin aiki na gargadi na kwana bakwai, sun janye yajin aikin, inda suka ce ana ta musu barazana.

10. Ma’aikatan kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya na ci gaba da yajin aiki a kan wasu bukatunsu har da ariyas na sabon albashi.

11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a da ma’aikata ma na bin bashin albashin kusan wata hudu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na san za a yi mamaki idan na ce sau daya na taba shiga Fadar Sarkin Zazzau a rayuwata. Ita ma na je dauko rohoto ne na nadin Iman Balele Wali a matsayin Limamin Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna shekarun baya da nake aiki da gidan talabijin na jihar Kaduna. Ikon Allah na manta shekarar kuma jiya har kiran dan Imam Balele Wali wato Yusuf Balele Wali, da yake tare muka yi karatu a C.A.S. Zariya a 1986 zuwa 1988 a waya na yi, don ya tuna mun shekarar ya ce ya manta.
Allah Ya jikan Mai Martaba Sarkin Zazzau Dafta Shehu Idris, da sauran iyayenmu da suka riga mu gidan gaskiya Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply