Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21.11.2020

Taskar Guibi: 21.11.2020

392
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, biyar ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Nuwamba na shekarar 2020.

1. Gwamnatin Tarayya dai ta yi amai ta lashe a tirka-tirkarta da malaman jami’a. Domin kuwa dole ta jingine IPPIS gefe guda, za ta biya malaman duk albashin da suke bi, tun daga watan Maris da ta dakatar da albashin nasu zuwa yau, ta amfani da tsohuwar hanyar biyan albashi ba IPPIS ba. Sannan Gwamntin Tarayya ta kara musu yawan kudin da ta musu alkawari tun farko suka ce ba su yarda ba. Ta amince ta musu karin, da ya zama za a ba su Naira Biliyan 65 ke nan. Sai dai shugabannin kungiyar malaman sun je su sanar da ‘ya’yan kungiyar yadda suka yi da Gwamnatin Tarayya. Idan sun amince su janye yajin aikin. Idan ba su amince ba, su koma su sanar da Gwamnatin Tarayya. Sai dai alamu na nuna za su janye yajin aikin zuwa makon gobe.

2. Kungiyar Dalibai da ke karatun aikIn lauya a jami’o’i ta kasa ta kai malaman jami’a da ke yajin aiki kara kotu, tana neman malaman su biya daliban Naira Biliyan Goma, saboda kin koyar da su, wanda tamkar tauye musu hakkinsu na a koyar da su ne, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar nan.

3. Kungiyar Dalibai Reshen Arewa, ta ba malaman jami’a mako daya, ko dai ta janye yajin aikin da take yi, ko su kai ruwa rana da malaman.

4. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce idan aka soke Majalisar Dokoki kamar yadda wasu ke ta kira a yi, to za a auka cikin rudani. Ya ce dududu kasafinsu a cikin kasafin kasar nan na 2021 bai wuce kashi daya ba cikin kashi dari na kasafin Nijeriya da har ake zarginsu da wawure dukiyar kasa ta kasafinsu. Ya ce a mako na biyu na waran gobe za su amince da kasafin kudi na shekarar 2021.

5. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce an ceto ‘yan sanda tara daga cikin guda goma sha biyu masu mukamin ASP da kidinafas, suka yi kidinafin a hanyarsu ta zuwa Zamfara daga Barno.

6. Mai shari’a mai ritaya Salami ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoton kwamitinsa na shari’a da ya binciki Ibrahim Imagu, har ya ba da shawarar ya kamata nan gaba idan za a nada sabon shugaban hukumar EFCC, a dinga daukowa daga cikin jami’an hukumar ta EFCC ko daga sauran hukumomin tsaro ba sai lallai dan sanda ba. Ya ce tun da aka kafa hukumar dan sanda ake nada mata.

7. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 143 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 70
Kaduna 25
Abuja 22
Ogun 11
Filato 4
Oyo 4
Ekiti 3
Oshun 2
Edo 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 65,982
Jimillar da suka warke 61,782
Jimillar da ke jinya 3,035
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,165

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, Mohammad Adamu, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin tsaro a lokacin shagulgulan karshen shekara da ke karatowa.

10. Al’umar Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A gobe lahadi idan Allah Ya kai mu, za a buga kwallon kafa tsakanin ma’aikatan DITV/Alheri Rediyo, da ma’aikatan Kasteliya da karfe hudu na la’asar a babban filin wasa na Ahmadu Bello da ke cikin garin Kaduna. Na dai ba da shawarar kada a yi wa kasteliya ci da daya. Don idan aka musu ci da yawa, to duk ma’aikatan DITV/Alheri Rediyo da ke da abin hawa sun shiga uku.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply