Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 21:05:2020

Taskar Guibi: 21:05:2020

235
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da takwas ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagorancin Taron Majalisar Zartaswa ta Kasa na larabar nan, kuma a cikin abubuwan da taron ya cimmawa, har da wata naira miliyan dari da daya da za a ba kwalejin koyar da tukin jiragen sama wacce ke Zariya.

2. Majalisar Dattawa ta nemi lallai a kwace wutar lantarki daga hannun wadanda suka sayeta saboda sun gaza.

3. Ma’aikatan wutar lantarki bangaren dakonta wato TCN a takaice, sun soma bore saboda tsige musu babban shugaba, da maye gurbinsa da wani da gwamnatin tarayya ta yi.

4. Gwamnatin Tarayya ta zaftare albashin ma’aikatan tashoshin jiragen sama na kasar nan.

5. Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin Tarayya ta mayar da ma’aikata da aka kora su dari hudu da saba’in daga matatar mai ta Warri da Kaduna, bakin aikinsu.

6. Kwalejin horas da kananan hafsoshin soja da ke Kaduna NDA ta kori wasu dalibanta su goma sha uku, ta yi wa daya dimoshan saboda magudi bangaren jarabawa.

7. Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa NAFDAC a takaice, ta ce yanzun akwai magunguna guda hudu a hannunta da take gwada ingancinsu wajen warkar da kwaronabairos.

8. An kwaso ‘yan Nijeriya da ke Saudiya su dari biyu da casa’in da biyu, an kuma killace su a Abuja. Sai dai wadanda ke Masar su fiye da dari hudu na rokon su ma a hanzarta kwasosu don wasunsu sun je can jinya ne sai ga kwaramniyar kwaronabairos ta ritsa da su a can.

9. Wasu malamai da masu yaki da kwarona sun ce sam ba su ji dadin damar da gwamnatin jihar Kano ta bayar, ta a yi Sallar Juma’a da ta Idi ba.

10. Gwamnatin jihar Bauci ta ba da damar a yi Sallar Juma’a da ta Idi.

11. Kungiyar Ma’aikatan Lafiya Reshen Jihar Kaduna, ta ba Gwamnatin Jihar Kaduna sa’a arba’in da takwas ko ta mayar musu da kudinsu kashi ashirin da biyar da ta yanke musu daga albashi, ko su kai ruwa rana da ita.

12. Sojojin sama na Nijeriya sun lalata wadansu kayan aiki na kungiyar Boko Haram da ke Njimia a jihar Barno.

13. Kungiyar malaman kwalejojin foliteknik ASUP a takaice, na nan tana shirin tsindima yajin aiki bayan an kwaranye da kwaronabairos saboda yadda ta kasa gane tsarin nan na IPPIS. Ta yi korafin albashin ‘ya’yan kungiyar na ta ciwon kai, har kwaronabairos ma ta taba albashin wasu yana can a killace.

14. Malaman jami’o’i da dama na gwamnatin tarayya, har yau ba su ga albashinsu na watan Fabrairu da Maris ba, ballabtana na Afrilu, ga Mayu na shirin mutuwa.

15. Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bai wa musulmi shawarar a soma duban jinjirin watan Shawwal.

16. Kidinafas sun sako Hakimin Gwaraji da ke jihar Kaduna.

17. Yau ma akwai walwalar fita sayen kayan abinci a jihar Kaduna. Sai dai ana zargin a jiya da ake da walwalar wasu masu kayan damara koraye na dukan gwarawa da ke sayar da doya a wuraren bakin dogo da ke kusa da kasuwar Ceceniya a Kaduna. Har an ji daya daga cikin gwarawan tana fada wa mai dukan nata cewa ta fa haife shi yake dukanta don ta fito neman abinci.

18. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce abin yana ba ta mamaki a ce duk da kullen da aka sa jama’a amma kwaronabairos sai karuwa take yi kamar ruwan dare.

19. Kasar Caina/Sin ta ce ta gano maganin kwaronabairos da ke yi wa cutar kisan mummuke.

20. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci akwai mutane sabbin harbuwa da kwaronabairos su 284 a jihohi kamar haka:

Legas 199
Ribas 26
Oyo 19
Abuja 8
Barno 8
Filato 7
Jigawa 6
Kano 5
Abiya 2
Ekiti 1
Delta 1
Kwara 1
Taraba 1

Da ke nuna kowacce jiha tana da:

Legas 2954
Kano 847
Abuja 435
Katsina 281
Barno 235
Bauci 224
Jigawa 211
Ogun 178
Oyo 162
Kaduna 162
Gwambe 136
Edo 119
Sakkwato 113
Ribas 79
Zamfara 76
Kwara 66
Filato 56
Osun 42
Nasarawa 34
Kabbi 32
Yobe 32
Delta 28
Adamawa 26
Neja 22
Ekiti 20
Ondo 20
Akwa Ibom 18
Taraba 18
Inugu 16
Ebonyi 13
Abiya 7
Bayelsa 7
Imo 7
Anambra 5
Binuwai 5
Kogi 0
Kuros Ribas 0

Hukumar yaki da yaduwar miyagun cututtuka ta kasa ta ce ta yi kuskure a alkaluman da ta bayar ranar 18 ga watan nan na jihar Zamfara, da ta ce akwai sabbi takwas da suka harbu. To ba kowa da ya harbu ranar a Zamfara.

Jimillar wadanda suka harbu 6,677
Jimillar wadanda suka warke 1,840
wadanda suka riga mu gidan gaskiya 200
Wadanda ke jinya 4,637

Mu yi sahur lafiya, yini lafiya, buda baki lafiya.

Af! Wai guda 1,840 da aka ce sun warke ina aka samo maganin da aka ba su suka warke ne?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply