Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 22.02.2021

Taskar Guibi: 22.02.2021

89
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Litinin, goma ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Fabrairu, na shekarar 2021.

1. An sako daliban makarantar sakandare, da ma’aikatan makarantan da iyalansa da aka bi su har makarantar sakandare ta Kagara aka yi kidinafin.

2. An ceto fasinjojin nan su 21 da kidinafas suka yi kidinafin a motar hukumar sufuri ta jihar Neja, da har kidinafas suka fitar da hoton bidiyonsu, su dauke da rantsattsun makamai suna nuna wa duniya.

3. Shugaban Kasa ya jajanta tare da ta’aziya ga hukumomin sojan saman Nijeriya, sakamakon faduwar da wani jirginsu na sojan sama, mai suna Beechcraft King B350 ya yi a lokacin da yake kokarin komawa tashar jiragen sama ta Abuja, bayan tashinsa da wasu mintoci, sojojin da ke tuka shi suka ankara yana da matsala, suka yi kokarin komawa tashar. Ya fado da sojoji bakwai, kuma duk sun riga mu gidan gaskiya. An ce jirgi ne da ya tashi zai kama hanyar Minna, don kai dauki wajen ceto daliban makarantar Kagara.

4. Babban Hafsan Hafsosin mayakan kasa na kasar nan, Ibrahim Attahiru, ya ba sojojinsa wa’adin sa’a 48 su kwato masa garin Marte da wasu garuruwan uku, da ke hannun kungiyar Boko Haram.

5. Makasa da kidinafin sun kashe uba da dansa, suka yi kidinafin mutum tara yawanci mata da yara a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

6. Makasa da kidinafin, sun kashe mutum uku a yankin karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

7. Makasa da kidinafin sun jidi mutum 13 a yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

8. Gwamnatin Tarayya, da Kungiyoyin Kwadago, sun ci gaba da tattaunawa jiya da maraice, a kan karin kudin fetur da na lantarki.

9. Gwamnatin Tarayya ta dage haramcin zirga-zirga da ta yi wa jirgin Boeing 737 sakamakon mugun hadarin da samfarinsa ya yi a Indoneshiya da Itofiya.

10. Yau dukkan ‘yan makarantan boko da na Islamiyya ke komawa makaranta a jihar Kaduna.

11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

12. Masu raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos, sun raba 521 jiya, ga jihohi kamar haka:

Legas 166
Ogun 52
Ribas 47
Adamawa 37
Ebonyi 37
Akwa Ibom 25
Oshun 21
Bayelsa 18
Kaduna 17
Oyo 16
Abuja 15
Ekiti 14
Kano 12
Edo 12
Barno 9
Yobe 8
Ondo 6
Nasarawa 4
Bauci 2
Kwara 3

Jimillar da aka raba wa jihohi zuwa yanzun 152,074.
Jimillar da aka raba wa majinyata zuwa yanzun 128,619
Jimillar da aka raba wa matattu zuwa yanzun 1,839
Jimillar da aka raba wa majinyata 21,616.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wani rabutu da na yi ranar 21 ga watan Fabrairu na shekarar 2014, jiya shekarun rubutun bakwai daidai kamar haka:

“Da yake yau ce ranar harshen uwa a duniya wato WORLD MOTHER TONGUE DAY, Akwai rubuce-rubuce da na yi akan muhimmancin harshen uwa ga yaro, musamman Hausa. Ga duk wanda yake so ya karanta su zai iya tintiba ta. Ko ya nemi jaridu, da mujallu, da kasidu don karanta wadannan bayanai. Kokari ne na Kamfanin Guibi-Hausa Consultancy Services. Na baya-bayan nan shi ne wanda jaridar Leadership ta Hausa ta makon jiya ta buga a shafinta na 29”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply