Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 22.11.2020

Taskar Guibi: 22.11.2020

567
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, shida ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 246 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 66
Filato 63
Abuja 48
Kaduna 21
Bayelsa 19
Ribas 12
Neja 9
Ogun 4
Ekiti 2
Bauci 1
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 66,228
Jimillar da suka warke 61,884
Jimillar da ke jinya 3,178
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,166

2. Ana nan ana ci gaba da matsa wa Jonathan tsohon shugaban kasa, ya fito takarar neman shugabancin kasar nan a zaben 2023.

3. Sojoji sun sake halartar gaban kwamitin bincike na jihar Legas, inda suka bayyana cewa tabbas sun je wajen masu zanga-zanga a Lekki, kuma sun je ne saboda bata-gari ba saboda masu zanga-zangar ba. Kuma tabbas sun je da harsashi mai rai da harsashi mara rai, amma ba su harbi kowa da harsashi mai rai ba.

4. Wani taro da manyan mukarraban Gwamnatin Tarayya, da Ministoci da ‘Yan Majalisa, da Gwamnonin da ‘Yan kwangilar hanyar Abuja zuwa Zariya zuwa Kano, da aka yi a nan Kaduna, na cewa sai nan da shekarar 2025 za a kammala aikin hanyar.

5. Tattalin Arzikin Nijeriya ya sake shiga cikin mawuyacin hali wato RECESSION.

6. Dakarun soja da ke sintiri a titunan bayan garin Rigasa da ke jihar Kadun na cewa sun ceto mutum biyu Sahabi da Aliko, sai Sani da har yanzun ba su san inda yake ba, sai kuma wani da tsautsayi ya sa harsashi ya same shi ya rasu, bayan sojojin sun mayar da martanin wani farmaki da ‘yan bindigan suka kai wa jami’an tsaro. Da ma wasu bayanai na cewa mahara sun kai hari bayan garin Rigasa har suka yi sanadiyyar rai shekaranjiya juma’a.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

8. An zuba sojoji da sauran jami’an tsaro birjik a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, sai dai har yanzu ‘ya’yanmu wato daliban jami’ar Ahmadu Bello Zariya, na dajin a hannun kidinafas. A cikinsu akwai danmu Aliyu Sabitu Idris daga cikin garin Kudan, dan gidan Sabitu Sani, da ke a kan hanyarsu ta zuwa Legas, kidinafas suka kama su a hanyar Abuja.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya a shirin BBC Hausa na bayan asubah, na ji suna tambayar kwamishinan wasanni na jihar Kaduna, cewa wasu suna korafin matsalar tsaro na addabar jihar Kaduna, ku kun bushe da shirya guje-guje. Sai ya ce ai bikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Sai wani makwabcina da muke tsaye muna saurare ke cewa “Asshha, yanzun da ‘ya’yan kwamishinan ne ke hannun kidinafas, ko wasu nasa kidinafas suka kashe anya zai iya furta kalaman bikin Magaji ba ya hana na Magajiya su fito har da shi ana guje-guje a cikin garin Kaduna kuwa?”

Yanzun karfe hudu da rabi na asubah.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply