Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 22.12.2020

Taskar Guibi: 22.12.2020

384
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, bakwai ga watan Jjmada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Nuwamba, 2020.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 356 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 79
Legas 59
Kaduna 56
Katsina 37
Nasarawa 30
Kano 25
Edo 18
Gwambe 14
Kabbi 12
Akwa Ibom 7
Ribas 7
Sakkwato 7
Abiya 3
Ogun 1
Kuros Ribas 1
Jimillar da suka harbu 78,790
Jimillar da suka warke 68,480
Jimillar da ke jinya 9,033
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,227

2. Gwamnatin Tarayya ta ce wadanda ba su iya hada lambarsu ta shaidar dan kasa da layinsu na waya ba, an kara musu har zuwa 19 ga watan gobe. Wadanda kuwa ba su ma da lambar shaidar dan kasa, an ba su har zuwa 9 ga watan Fabraru, su je su yi rajistar ta dan kasa, su kuma hada lambar ta dan kasa da layin wayarsu.

3. Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun amince da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira Tiriliyan kusan 14.

4. Gwamna Zulun na jihar Barno ya ce gaskiya sojoji da ‘yan sanda da aka tura kare rayuka a jiharsa sun ba shi kunya. Ya yi zargin ba abin da suka iya sai sa shingen bincike suna karbar taro sisi da kwandala a hannun masu ababen hawa, amma ba sa iya kare su daga hannun kungiyar Boko Haram a jihar.

5. Sojojin sama sun ce sun samu karin wata nasarar ta lalata motocin yaki da kashe mayakan Boko Haram da dama a dajin jihar Barno.

6. Wani rahoton na cewa sojoji biyar aka kashe a wani harin na Boko Haram a jihar Barno.

7. Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe makarantu, har sai sha 18 ga watan gobe, saboda kwaronabsiros. Ta kuma bukaci a dinga rage cunkushewa waje guda har fiye da mutum hamsin a lokaci guda, a bukukuwa ko suna ko wuraren ibada.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin sun kusan cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo ga shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ta dauka nagyara musu gada tun lokacin yakin neman zabe. Ya ce idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

10. Malaman jami’a sun ce Gwamnatin Tarayya suke jira ta ce wani abu, sai su ma su ce wani abu, ko a samu dalibai su ma a ce musu wani abu a kan komawa makaranta.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Talaka na ci gaba da biyan kudin zama a duhu. Wutar a kullum sai kara tabarbarewa take yi. Ba a ba ka wutar ba, wata ya kare a kawo maka takardar kusan naira dubu talatin, ka je ka biya kudin zama a duhu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply