Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 23.02.2021

Taskar Guibi: 23.02.2021

31
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma sha daya ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Fabrairu, shekarar 2021.

1. Masu kaso da raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos, jiya sun raba wa jihohi alkaluma 542 kamar haka:

Legas 99
Kwara 91
Ebonyi 48
Ogun 44
Kaduna 42
Oyo 33
Ondo 25
Abuja 24
Kabbi 23
Oshun 20
Ekiti 17
Nasarawa 12
Imo 11
Delta 10
Gwambe 9
Kano 8
Katsina 7
Ribas 7
Edo 5
Filato 4
Bauci 3

Jimillar da aka hankada wa Nijeriya zuwa yanzun 152,616
Jimillar da aka hankada wa wadanda aka ce sun warke, 128,300
Jimillar da aka hankada wa wadanda aka ce suna jinya 23,154
Jimillar da aka hankada wa matattu 1,862

2. Gwamnatin Tarayya ta dauki alkawarin nan da mako biyu wato kwana goma sha hudu, za ta magance matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

3. Kungiyoyin Kwadago sun ce ba su yarda da yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na kara kudin miya zuwa naira dari biyu da ‘yan kai kowacce lita ba.

4. A Kano ‘Yan A Daidaita Sahu wato Nafef, sun soma wani yajin fita daukar fasinja daga jiya Litinin, don kin amincewa da wata naira dari da KAROTA ta sa wa kowanne dan Nafef zai dinga biya a kullum ya fita aiki

5. A jihar Zamfara wasu makasa kuma kidinafas su uku, sun fice daga sana’ar ta kisa da kidinafin, sun ajiye makamai.

6. Gwamnan Jihar Binuwai Ortom, ya yi zargin Fulani sun aike masa da takardar barazanar sai sun kashe shi, tare da zargin har da hannun takwaran aikinsa na jihar Bauci Gwamna Bala Mohammed. Saboda zargin da Ortom ya yi cewa ai shi Bala Mohammed ne ya nuna bafulatani yana da gaskiya idan ya dauki bindiga AK47, yana yawon kiwo da ita domin kare kansa da dukiyarsa. Ortom ya yi zargin cewa idan an ga an kashe shi to da hannun Bala Mohammed.

7. Sanata Okorocha na zargin gwamnan jihar Imo ta hannun sakatarensa, da mukarrabansa, da ‘yan daba, da ‘yan sanda ga dukufa ga cin zarafinsa.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka dade da biyan sauran ma’aikata, su kuwa har yau shiru.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya wasu daga cikin masu bibiyar rubutuna sun yi tsokacin sun ga ban yi korafin da na saba yi kullum a kan gadar kauyenmu Guibi ba. Suna tambayar ko an gyara ne ko kuma mun sasanta da shugaban karamar hukumar Kudan ne. To gada dai na nan ba a gyarata ba. Amma na hadu da daya daga cikin shugabannin karamar hukumar ta Kudan a masallaci, inda yake ce mun sun fara aikin gadar a can baya, sai kudi suka yanke musu. A yanzun haka ma, wanda suka ba kwangilar aikin gadar na bin su naira miliyan biyar. Ya ce so suke idan sun yi ta-zarce, suna sa ran lokacin za a samu kudi, sai a je a gyara gadar ta Guibi. Ya ce su ba su yi fosta da gadar Guibi suna neman ta-zarce ba. Na ce masa na ga fosta da idona. Ya ce su ba su yi wa mutanen Guibi alkawarin za su gyara musu gada ba. Na kira mutane Guibi a waya, suka ce har wajen gadar suka je da shugaban ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Wannan ya sa jiya na dan tsahirta da korafin saboda shekaranjiya a sallar magrib muka hadu ya mun wadannan bayanan. Matsalar irin wannan korafin da nake yi kullum, duk ranar da ban yi ba, za a ce ko dai an gyara gada, ko an gyara aljihuna. Ko korafin da nake yi a kan ariyas na ma’aikatan foli, rannan da ban yi ba, sai wasu daga cikin ma’aikatan suka soma tambayata, na ga nawa ariyas din ne ko dai an saye ni in daina maganar ne?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply